Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 A Kasar Australiya
Published: December 15, 2025 at 6:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan sanda a kasar Australiya sun ce ‘yan bindigar da suka kashe mutane 15 a wurin wani bikin yahudawa a gundumar Bondi Beach dake bakin ruwa a Sydney, babban birnin kasar, wani uba ne da dansa.

An kashe uban mai shekaru 50 da haihuwa a wurin harin, yayin da dan nasa mai shekaru 24 ya ji mummunan rauni, yana kuma kwance a asibiti.

Jami’ai sun fadawa manema labarai a ranar litinin cewa harbe-harben na jiya na nuna kin jinin yahudawa ne.

‘Yan sanda suka ce har yanzu mutane 40 suna asibiti a bayan harin, cikinsu har da wasu ‘yan sanda biyu da suka ji mummunan rauni amma suna murmurewa.

‘Yan sandan suka ce mutane kimanin dubu 1 ne suka hallara a wani wurin shakatawa dake wannan bakin gabar ruwa da yayi suna domin murnar bukin yahudawa na Hanukkah.

A halin da ake ciki, mutanen Australiya suna yaba ma wani farar hula da aka gani a cikin hotunan bidiyo ya kama dan bindigar da kokuwa, suna mai bayyana shi a zaman mutumin da ya ceci rayukan mutane da yawa. Gidan telebijin na Channel 7, yace wannan farar hula, wani mutumi ne dan shekara 43 mai suna Ahmed al Ahmed, wanda ke da wani kantin sayarda kayan marmari.

Hotunan bidiyo da aka yada ta kafofin sada zumunci na Intanet, sun nuna Ahmed sanye da farar riga ya labe a bayan wata mota dake kusa, ya sulalo bayan dan bindigar ya kwace makamin daga hannunsa.

Wani dan’uwan wannan mutumin da shugabannin Australiya da na kasashen waje ke bayyanawa a zaman gwarzo, yace an harbi Ahmed a hannu da kuma a damtsensa sannan kuma Shi ma dan bindigar ya harbe shi har sau biyu, kuma yana asibiti an yi masa tiyata.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka
Next Post: Sabon Ma’aikacin Tsaro Ne Ya Kashe Amurkawa

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin Labarai
Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
  • Rasha Ta Gargadi Amurka Da Isra’ila Kan Harin Iran Afrika
  • Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
  • Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine Labarai
  • Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
  • Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
  • Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.