Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara
Published: February 21, 2026 at 5:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A kalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai wani kauye a jihar Zamfara, tare da sace mata da yara da yawa, a cewar wani dan majalisa da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Jumu’a.

Hamisu A Faru, dan majalisa mai wakiltar Bukkuyum ta kudu ya ce, ‘yan ta’addan sun far ma kauyen Tungan Dutse wajen karfe biyar na yamma ranar Alhamis, suka ci gaba da tafka barna har zuwa 3:30 na wayewar safiyar Jumu’a, inda suka kokkona gidaje, suka kuma rika harbin mutanen da ke guduwa don tsira da ran su.

Ya ce har yanzu ba’a san adadin mutanen da aka sace ba.

Wani mazaunin wurin Abdullahi Sani, ya ce kwana daya kafin faruwar abun mazauna kauyen sun tuntubi jami’an tsaro lokacin da suka ga babura fiye da 150 dauke da mutane, amma babu abin da aka yi a kai.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kotun Amurka Ta Soke Harajin Fito Da Shugaba Trump Ya Kakabawa Kayan Kasashen Waje
Next Post: Fiye Da Mutane Miliyan Hudu Suna Fuskantar Barazanar Yunwa A Somaliya

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami Najeriya
Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
Mutane Biyu Sun Mutu A Yayin Zaben Shugabannin Gundumomin APC A Jihar Ondo Najeriya
Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Kano Da Katsina Tsaro
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
  • Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Najeriya
  • Sojin Ukraine Sun Janye Daga Gabashin Kasar Amurka
  • Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine Labarai
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.