Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika

‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u
Published: May 4, 2026 at 11:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya jaddada shirye-shiryen rundunar ‘yan sanda wajen magance munanan dabi’u a tsakanin matasa a fadin jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron hulɗa da al’umma da wayar da kai kan yaƙi da munanan dabi’u ta hanyar aikin ‘yan sanda wanda aka gudanar a Gombe International Hotel.

Ya ƙara da cewa yana da tsare-tsare na ƙarfafa aikin ‘yan sanda na rigakafi ta hanyar haɗin gwiwa da shugabannin addinai, shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki.

A saƙonnin fatan alheri, Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN a jihar Gombe, Reverend Joseph Alphonsus Shenga, da Shugaban Jama’atu Nasril Islam a jihar, Alhaji Saleh Danburam, tare da Ibrahim Yusuf 3000, sun ba da tabbacin goyon bayansu ga shirye-shiryen Kwamishinan ‘yan sanda na yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi, daba, da kuma inganta tsaron al’umma ta hanyar aikin ‘yan sanda na rigakafi.

Sun kuma yaba da jajircewar Kwamishinan ‘yan sandan tare da kira ga samar da isassun jami’an tsaro a muhimman sassan jihar domin ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro.

Da yake nasa jawabin, mai riƙe da sarautar Wazirin Yeriman Gombe, Alhaji Yaya Hammari, ya yi bayani kan tarihin aikin ‘yan sanda a jihar, inda ya yaba da ƙirƙirar wannan taro na hulɗa da al’umma wanda zai taimaka wajen rage munanan dabi’u.

Ya bayyana cewa shan kayan maye a tsakanin matasa na haddasa rashin aikin yi da sauran matsaloli a cikin al’umma, tare da kira ga bayar da cikakken goyon baya da haɗin kai domin samun nasara.

Shi ma Shugaban PCRC na jihar Gombe, Kwamared Garba Ubale, ya ce wannan shiri na Kwamishinan abin a yaba ne, yana mai cewa wannan shi ne karo na uku da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin CP Ahmed Chuso.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin DPO na Pantami bisa fahimta da jajircewa, tare da kira da a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da munanan dabi’u domin ci gaban al’umma.

A nasa ɓangaren, Abdulaziz Sani Labaran na Youth O’Clock, a cikin takardar da ya gabatar, ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa da wasu na taimakawa wajen jefa matasa cikin shan kayan maye, inda ya buƙaci a ɗauki matakan da za su kawo ƙarshen lamarin.

A takardar daya Gabatar Malami Daga Sashin ilimin halayyar Dan Adam na jami’ar jihar Gombe Dr. Ahmad Adamu ya bayyana aikin tsaro a matsayin Wani muhimmin aiki Wanda yake taimakawa Wajen kyautata rayuwar al’umma.

Dr. Ahmad Yace akwai kwarewa tare da salo ayyukan Jami’an Tsaro Wajen Kawo Karshen matsalar Tsaro a cikin al’umma, inda ya bukaci Samun hadinkan al’umma wajen Samun nasarar Abunda aka Saka a gaba.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe
Next Post: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina

Karin Labarai Masu Alaka

Fitaccen Dan Jarida a Sokoto Surajo Dalhatu Sifawa Ya Rasu Najeriya
Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
Tsarin Haraji Mai Cike Da Ayoyin Tambaya Na Shirin Fara Aiki Labarai
Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Djibouti Yau Juma’a Afrika
Duk Da Rauni Daya Samu Sakamakon Hari Mojtaba Khameni Yafara Aiki Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
  • Yawan Mai Da Kasashen OPEC Suke Hakawo Yayi Kasa Sosai Labarai
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.