Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai
Published: January 15, 2026 at 9:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan sanda a Habasha ko Ethiopia sunce sun kama dubban albarusai da Eritrea ta aikawa ‘yan tawaye a yankin Amhara, zargin da Eritean tayi watsi da shi a zaman kariya da Ethiopia ta zuka da nufin kafa hujjar ta afka yaki.

Zargin da rundunar ‘Yansandan kasar Ethiopia tayi ya zafafa rikici tsakanin kasashen biyu, da suka jima suna gaba da juna, amma suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya a 2018, wadda tuni sabbin barazana tsakanin kasashen biyu yake maye gurbinta.

A cikin sanarwar data bayar a daren ranar Laraba, rundunar ‘Yan sandan a habashan tace ta kama albarusai dubu 56,000, ta kama mutane biyu a yankin Amhara cikin makon nan, yankin da kungiyar ‘yan tawaye da ake kira Fano take kaddamar da hare hare da turjiya tun a shekarar 2023.

Ministan yada labarai a Eritrea Yemane Gebremeskel, ya fadawa kamfain dillancin labarai na Reuters cewa, jam’iyyar PP ta PM Abiy Ahmed, tana neman wata hujjar da zata fake dashi domin ta kai farmaki.

Tunda a farkon wannan mako a hira da yayi a kafofin yada labaran Erirea, shugaban kasar Isaias Afwerki, yace jam’iyyar PP a Habasha ta ayyana yaki kan kasarsa.

Kasashen biyu sun gwabza yaki kan rikicin kan iyaka rikici da ya barke a shekara ta 1998, shekaru biyar bayan da Eritrea ta sami ‘yancin kai daga kasar Habasha ko Ethiopia.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ghana Tayi Watsi Da Yarjejeniya Akan Hakar Ma’adanai
Next Post: Shugaba Trump Yayi Barazanar Tura Sojoji Ga Masu Zanga Zanga

Karin Labarai Masu Alaka

Magoya Bayan Tijjaniyya Zasu Kauracewa Zabe Saboda Kama Sheikh Sani Khalifa Afrika
Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Talauci Ya Ragu A Tsakanin Al’ummar Jihar Jigawa Siyasa
  • Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
  • Sabon Magajin Garin New York Zai Soke Wasu Dokoki Amurka
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Eberechi Eze Ba Zai Buga Wasannin Da Ingila Za Tayiba Arteta Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.