Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Yawan Mai Da Kasashen OPEC Suke Hakawo Yayi Kasa Sosai
Published: February 10, 2026 at 10:36 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 10, 2026

Yawan mai da kasashe dake kungiyar OPEC masu arzikin mai suke hakowa yayi kasa sakamakon karancin mai da Najeriya da Libya suke hakowa, kamar yadda wani bincike da kamfanin dillancin lbarai na Reuters ya gano Ranar Litinin.

Kasashe da suke cikin kungiyar OPEC suna hakar mai ganga milya 28.34 ako wace rana cikin watan Junairun da ya wuce, wanda ya nuna koma baya da kamar gangar mai dubu 60 idan aka duba alkaluman watan Disamba binciken ya nuna, Najeriya ce ta sami koma baya sosai a yawan abunda take hakowa.

OPEC da kasashe kawayenta da suka hada da Rasha sun fara rage hanu a watanni uku na farkon shekara na yawan mai da suke hakowa saboda fargabar suna iya fuskantar kwanten mai a duniya.

Karkashin wata yarjejeniyar da kasashe 8 da suke cikin kungiyar da wasu kawayenta ba zasu kara yawan abunda suke hakowa ba a watan jiya, sun hada da Aljeriya, da Iraq, da Kuwait, da saudi Arabia, da hadaddiyar daular larabawa, gabannin ganin tasirin rage abunda suke hakowa da adadinsa ya kai gangan dubu 130, da zai shafi Iraqi da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Najeriya ce dai aka ga matukar koma bayan mai da take hakowa, da kuma Libya, wacce ta fuskanci matsalar yanayi wadda ya shafi lodin manta.

Haka nan an sami koma bayan mai daga Iran sosai, saboda Amurka tana kara mata takunkumi game da shirin Nukiliyar kasar.

Sai dai binciken bai fadi matsalar data sa Najeriya ta sami koma bayan mai da take hakowa ba.

A halinda ake ciki kuma, farashin mai ya tashi da kamar kashi daya, bayanda Amurka ta gargadi jiragen ruwa suyi taka tsantsan kusa da Iran.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC
Next Post: Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC Labarai
Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
Kasar Jamus Ta Haramtawa Yara Kasa Da Shekaru 14 Hawa Dandalin Sada Zumunta Labarai
Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Birtaniya Zata Fara Raba Rigakafin Allurar Cutar Sankara Kimiya
  • Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
  • Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
  • CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
  • Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika
  • Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.