Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Horar Da Matasa Sama 7,000 A Matsayin Masu Tsaron Daji
Published: December 27, 2025 at 6:35 PM | By: Bala Hassan

Gwamnati Ta Kammala Horar da Sama da Matasa 7,000 a Matsayin Masu Tsaron Daji Da Za a Tura su Aiki Nan take

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala horar da fiye da matasa 7,000 da aka dauka a matsayin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a jihohi bakwai da ake ganin suna fuskantar matsanancin barazanar tsaro.

Wannan horo ya gudana ne karkashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kaddamar a watan Mayu na shekarar 2025 domin dawo da ikon gwamnati a cikin dazuzzuka da ke kara zama mafakar ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

An gudanar da bikin yaye daliban a ranar 27 ga Disamba, 2025 a jihohi Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi, inda kowane bangare na horon ya kasance mai tsauri da tsari, domin gina dakaru masu kwarewa da jajircewa wajen aikin cikin daji da wuraren da ba a iya shiga cikin sauki.

A bayanin da ya gabatar a bikin yaye su, Mai Ba Da Shawara kan Tsaron Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana shirin a matsayin “mataki mai karfi” wajen dawo da zaman lafiya da kare al’ummomi.

“Wadannan Masu Tsaron Daji ba kawai ma’aikata bane da suka sa kaya. Su ne masu kare al’umma, masu tarin bayanai, kuma ginshiki a cikin tsarin tsaronmu. Za su tsaya a kasa, su wanke wuraren da masu aikata laifi ke buya, su kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen kwato yankunan da miyagu suka mamaye,” in ji shi.

Ya kara da cewa, babu wani tazara tsakanin kammala horo da fara aiki:

“Nan da nan za a tura su bakin aiki, albashinsu da hakkokinsu za su fara nan take.”

An shafe watanni uku ana horar da wadanda aka dauka, inda aka mayar da hankali kan:

Horon jiki da kwakwalwa (physical & mental endurance)

Tsallake cikas, da hanyoyin jure doguwar tafiya cikin daji

Horar da su kan dabarun yaki da tsari na tsaro (tactical drills)

Horo kan mayar da martani yayin farmaki, da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su

Horon kyakkyawar mu’amala da fararen hula, kare hakkin bil’adama, da bin doka

Daga cikin wadanda suka halarta horon, kashi 98.2 cikin ɗari ne suka kammala. An kori mutane 81 sakamakon kin bin ka’ida, yayin da biyu suka rasu saboda matsalolin lafiya. Mafi yawansu ’yan asalin yankunan da za su yi aiki ne, abin da gwamnati ta ce zai taimaka musu wajen sanin daji, hanyoyin shiga da fita, tare da samun goyon bayan al’umma.

Masu Tsaron Dajin na karkashin kulawar Ofishin Mai Bada Shawara kan Tsaron Kasa tare da Ma’aikatar Muhalli, karkashin daidaitawar DSS da Hukumar National Park Service. Haka kuma rundunar soji, rundunar sojin ruwan Najeriya, rundunar ’yan sanda da NSCDC duk sun bayar da gudummawa wajen tsari da dabarun aiki.

Gwamnoni da mataimakansu daga jihohin da abin ya shafa sun halarci taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayin da wasu jihohin suka samu wakilci daga mataimakan gwamnoni.

A karshe NSA Nuhu Ribadu ya sake jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da fadada shirin zuwa sauran jihohi:

“Idan muka kare dazukanmu, mun kare kasa. Idan muka kare kasa, mun kare rayukan al’ummanmu. Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba.”

Labarai

Post navigation

Previous Post: Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe
Next Post: Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a Labarai
Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
  • Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco Afrika
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
  • Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
  • Malaman Tsangaya A Gombe Sun Goyi Bayan Inuwa Yahaya Da Jamilu Gwamna Afrika
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.