Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai
Published: November 16, 2025 at 12:32 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Kasar Iran ta tabbatar a yau Asabar cewa dakarunta na juyin juya hali sun damke wani jirgin tanka da suka ce ya keta dokoki, wanda ke dauke da fetur a cikin tekun Gulf, wanda aka ce ya doshi kasar Singapore.

A jiya jumma’a ne jami’an Amurka da majiyoyin tsaron zirga zirgar jiragen ruwa suka ce dakarun Iran sun tare wannan jirgi suka juya akalarsa zuwa cikin yankin ruwan kasar Iran din.

Wannan shine karon farko da Iran take kama wani jirgin ruwa a cikin tekun Gulf tun cikin watan Afrilun 2024.

Gidan Talebijin na Iran ya karanta wata sanarwar da Rundunar Dakarun Juyin Juya Hali ta kasar ta bayar dake cewa,  jirgin ruwan tankar ya keta doka ta hanyar dauko kayayyakin da ba a amince da safararsu ba. Sanarwar ba ta yi karin bayani a kan wannan abu da ake zargi.

Wannan jirgin ruwan da Iran ta kama a mashigin ruwan Hormuz, ya yi lodi ne a Sharjah dake Hadaddiyar Daular Larabawa.

Iran dai ta dakile yawan ayyukanta na soja a yankin tun bayan dauki ba dadin da suka gwabza da Isra’ila da  Amurka a watan Yunin wannan shekara.

Labarai

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke
Next Post: Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba Afrika
Pakistan Zata Karbi Bakwancin Saudiya, Turkiyya Da Masar Afrika
An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
Karamar Sallah: Hukumar Kashe Gobara A Gombe Ta Kuduri Aniyar Kare Al’umma Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa Afrika
  • Borno: An Yi Kwanton Bauna Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Afrika
  • Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallar Azumi Afrika
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • An Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Birnin Niamey Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.