Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa
Published: January 8, 2026 at 7:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin, ya karyata zargin cewa majalisar dokoki ta ƙasa tana bin umarnin bangaren zartarwa ba tare da ‘yanci ba.

Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a Ilorin yayin da yake gabatar da laccar bikin yaye ɗalibai karo na 15 a Jami’ar Al-Hikmah, inda ya ce haɗin kai tsakanin majalisa da bangaren zartarwa an yi shi ne domin samar da kyakkyawan shugabanci.

Ya danganta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin bangarorin biyu da kwarewar Shugaba Bola Tinubu a matsayin tsohon gwamna kuma ɗan majalisa, yana mai cewa hakan ya ƙarfafa fahimta, sadarwa da shawarwari, musamman wajen gabatar da kudurorin dokoki.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wasu na kuskuren fassara wannan haɗin kai a matsayin majalisa ta zama “yar amshin shata” kawai, yana mai jaddada cewa haɗin kai ya fi rikici amfani ga ci gaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa dorewar dimokuraɗiyya na buƙatar bin kundin tsarin mulki, hikima da wayayyun ‘yan ƙasa masu kishin ƙasa.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi
Next Post: Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Shari’ar Abubakar Malami Ta Kaura Zuwa Sabon Alkali Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
  • Patrick Vieira Ya Cimma Yarjejeniyar Zama Sabon Kocin Senegal Wasanni
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
  • Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
  • An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
  • Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
  • Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.