Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro
Published: February 20, 2026 at 12:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da takwaran aikinsa na Jamus Chancellor Friedrich Merz, sun tattauna ta wayar tarho kan batun tsaro, makamashi lantarki, da kuma kayayyakin more rayuwa, kamar yadda ofishin shugaban kasan ya fada a ranar Alhamis.

A maganar da suka yi ranar Laraba, na tsawon minti tara, shugabannin biyu sunyi magana kan sake farfado da aikin samar da wutan lanatarki a Najeriya da ya tsaya, da babban kamfanin kasar Jamus SIEMENS zai yi, haka kuma Najeriya zata sayi jirage masu saukar ungulu wadanda ba sababbi bane daga Jamus.

Shugaba Tinubu ya gayawa Mr. Mertz cewa Najeriya tana bukatar taimako wajen sabunta hanyoyin samarda wutan lantarki a kasar.

Wata yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kamfanin SIEMENS a shekara ta 2019, kamfanin zai sabunta hanyoyin raba wutan lantarki da bankunan Jamus za su dauki nauyin aikin, da zimmar idan aka kamala aikin zai samar da wutan lantarki MegaWatts dubu 7, zuwa 2021, sannan ya karu zuwa megawatt dubu 11 zuwa karshen Shekara ta 2023, sai dai aikin ya fuskanci kalubale daban daban da suka hada da kudi, sharuddan gwamnati da makamantar su.

Shugaba Merz na Jamus ya fadawa shugaba Tinubu cewa kamfanin SIEMENS zai yi aikin, kuma a shirye Bankin Deutsche yake ya samar da kudaden tafiyar da aikin, kamar yadda sanarwa daga ofishin shugaban kasar ya fada.

Najeriya da Jamus suna da huldar difilomasiyya na tsawon shekaru 65.

Labarai, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Masu Hakar Ma’adanai 37 Sun Mutu A Jihar Filato
Next Post: Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki Afrika
Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
  • Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash Labarai
  • Kasar Spain Ta Rufe Sararin Saman Kasar Amurka
  • Nwakali Na Dab Da Komawa Kungiyar PAC Omonia Ta Cyprus Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.