Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa
Published: February 24, 2026 at 7:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

MDD da gwamnatin Somaliya sun fada Ranar talata cewa kimanin ‘yan kasar somaliyan milyan shida da rabi ne suke fuskantar ‘yunwa mai matsanani sakamakon fari, domin ko a makon jiya ma hukumar samar da abinci ta MDD tayi gargadin cewa tallafin abinci da take bayarwa a kasar zai tsaya cik cikin watan Afrilun bana, idan ba an sami karin kudi ba.

A sanarwa ta hadin guiwar MDD da gwamnatin somaliyan suka bayar, sunce fiye da rabin masu fuskantar matsanancin ‘yunwar yara ne, suka ce lamarin ya tilastawa dubban mutane su bar muhallansu suka shiga cikin tantuna a birnin Mogadishu da wasu birane.

A makon jiya, hukumar kula da abinci ta MDD ta ce mutane da suke fuskantar matsananciyar ‘yunwa sun kai milyan hudu da dubu dari hudu, kuma har ta rage yawan wadanda take tallafawa daga mutane milyan biyu da dubu dari biyu, zuwa dubu dari shida kacal daga farkon wannan shekara.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Babban Bankin Najeriya Ya Rage Kudin Ruwa Da Kashi Daya Cikin Dari
Next Post: Iran Da Amurka Zasu Cimma Yarjejeniyar Nukiliya

Karin Labarai Masu Alaka

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika
Fiye Da Mutane Miliyan Hudu Suna Fuskantar Barazanar Yunwa A Somaliya Sauran Duniya
Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Asusun IMF Zasu Ziyarci Kasar Gabon Afrika
  • Yawan wadanda suka mutu a mummunan harin yanbindiga a Jihar kwaran Najeriya yakai 170 Najeriya
  • Gwamnatin Tinubu Ta Warware Basussukan Fansho Na Shekaru 18 Afrika
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar Rumbun Hotuna
  • Baitul Malin Amurka Zata Bawa Venezuela Da Cuba Damar Sayar Da Mai Amurka
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.