Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Kasar Guinea Ta Soke Wasu Jam’iyyun Siyasa
Published: March 9, 2026 at 6:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin kasar Guinea ta soke jam’iyyun siyasa 40 a kasar, inda ta ce a wata doka da ta wanzar ranar Jumu’a za’a rufe duk manya da kananan ofisoshin jam’iyyun 40 a fadin kasar, kuma za’a haramta musu amfani da duk wata alama ko zane dake nuni jam’iyyar.

Dokar ta ce jam’iyyun sun kasa sauke hakkin doka, kamar aikewa da bayanan kudaden su. Da yawa daga cikin jam’iyyun sun koka da wannan hukunci, inda suka dage akan sun yi duk wani abu da doka ta tanada.

Babban dan jam’iyyar adawa a kasar ya ce turjiya kai tsaye ga shugaban kasar mai ci a yanzu ita ce kadai hanyar da za’a kawo sauyi.

Shugaba Mamady Doumbouya, wanda da soja ne, yayi juyin mulki a shekarar 2021, daga baya kuma ya ci zabe na zama shugaban kasa har zuwa shekaru 7 a watan Disamba, wanda sauran ‘yan takara suka kalubalanta. Ana sa ran yin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar a watan Mayu.

Afrika, Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya
Next Post: Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa

Karin Labarai Masu Alaka

An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika
Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • Shugaban Amurka Yace Zayyi Wahala A Cimma Yarjejeniya Tsakanin Isra’ila, Amurka Da Iran Amurka
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025. Wasanni
  • Fafaroma Leo Zai Ziyarci Kasashen Afirka Amurka
  • Gwamnatin Trump Tana Cigaba Da Korar Baki Daga Amurka Afrika
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.