Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa Afrika

An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran
Published: March 18, 2026 at 9:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A ranar Larabar ne aka kai hari kan babbar tashar iskar gas ta Pars a kasar Iran, wannan shine karon farko na kai hari kan kayayyakin makamashin Iran a mashigin tekun Fasha tun fara yakin Amurka da Isra’ila, lamarin da ya sa Tehran ta gargadi makwabtanta cewa za a kai hari kan na’urorin makamashin nasu “a cikin sa’o’i masu zuwa”.

Tashar Pars dai itace tashar iska mallakar Iran da take mafi girman tashar gas a duniya, wanda Iran ta raba da Qatar da ke gabar tekun Gulf. Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, an kai harin tankunan gas da wasu sassan matatar mai, an kwashe ma’aikata zuwa wani wuri don basu kariya, sannan kuma ma’aikatan gaggawa na kokarin kashe gobara.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun yi ta yada labarin cewa Isra’ila ce ta kai harin tare da amincewar Amurka. Sojojin Isra’ila ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.

Qatar, kawayen Amurka dake dauke da sansanin sojin saman Amurka mafi girma a yankin, ta kira harin da Isra’ila ta kai ba tare da ambaton wani rawar da Amurka ta taka ba. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta kira lamarin “mai hadari da rashin da’a” wanda ya jefa tsaron makamashin duniya cikin hadari.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun shaida wa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar da su kwashe inasu-inasu a wasu wuraren samar da makamashi.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi
Next Post: ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne Labarai
Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Kasar Kenya Zata Samar Da Makamashi Labarai
Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
  • Shugaban Amurka Zai Sake Gine Gaza Amurka
  • Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
  • Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
  • Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
  • Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
  • Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika
  • Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.