Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar
Published: March 27, 2026 at 8:37 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A ranar Alhamis, wani alkali a Amurka ya kalubalanci dalilin da yasa gwamnatin Amurka ta hana hambararren shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro amfani da kudi daga kasar sa domin biyan lauyoyin da zasu kare shi a kotu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da Amurkan ke masa. Amma alkalin ya ce ba zai yi watsi da tuhumar da ake masa ba saboda wannan dalili.

Maduro tare da mai dakin sa sun sa Cilia Flores, sanye da kayan kurkuku, sun gurfana a wata babbar kotu dake Manhattan a birnin New York, fiye da watanni biyu bayan da sojojin Amurka suka kamo su a wani samame da ya bada mamaki a fadar su dake Caracas, babban birnin Venezuela.

Maduro mai shekaru 63, da matar sa mai shekaru 69, sun nemi alkali yayi watsi da tuhumar da ake musu, inda suka ce rashin damar samun kudi daga Venezuela na kawo musu cikas wajen damar da suke da shi na daukan lauyan da suka zaba wanda hakan ke kunshe a cikin kundin tsarin dokar Amurka.

Sun Kuma musanta laifin tuhumar da ake musu na safarar mugayen kwayoyi. Ana ci gaba da tsare su a wani kurkuku a Brooklyn dake New York.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran
Next Post: Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
Magoya Bayan Tijjaniyya Zasu Kauracewa Zabe Saboda Kama Sheikh Sani Khalifa Afrika
Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi Afrika
Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
Lauyoyi Sun Gurfanar Da Wani A Kotu Bisa Fasa Korin Kiyashi A Kenya Afrika
Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Game Da Kisan Dorayi Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nada Jakadu Da Tinubu Yayi Sako Ne Ga ‘Yan-Arewa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
  • Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana Kimiya
  • Kungiyar Kiristoci Ta Wanke Gwamnan Bauchi Daga Zargin Ta’addanci Labarai
  • Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai
  • Afrika Ta Kudu Ta Dora Haraji Mai Yawa Kan Karafa Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.