Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus
Published: April 3, 2026 at 7:21 AM | By: Nasiru Adamu Elhikaya

Jam’iiyyar ADC Ta Bukaci A Sauke Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Amupitan

Gamayyar adawa ta jam’iyyar ADC ta bukaci murabus ko a sauke shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Joash Amupitan da kwamishinoninsa daga mukaminsu don ba su da kwarin guiwar za su gudanar da zabe mai adalci.

Bukatar ta fito ne a taron gaggawa na manyan ‘yan adawar karkashin jagoransu tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark.

“mu na bukatar murabus ko a sauke shugaban hukumar zabe da kwamishinoninsa don ba mu amince za su iya yi ma na adalci a babban zaben 2027 ba” Inji shugaban hadakar David Mark wanda ke martani mai zafi bayan matakin INEC na dakatar da amincewa da bangarori biyu masu da’awar hakkin shugabancin jam’iyyar.

INEC ta ce ta bi umurnin kotu ne wajen dakatar da karbar bayanai daga shugaban hadakar David Mark da kuma na bangaren turjiya Nafiu Bala sai an samu sabon umurnin kotu.

Mark ya ce ya kamata INEC ta jira sai kotun daukaka kara ta yi matsaya kan takaddamar, amma maimakon haka sai INEC ta bi muradun jam’iyyar APC mai mulki.

A nan Mark ya ce sun sanar da INEC gudanar da tarukan jam’iyya daga 9 ga watan nan na Afrilu inda zai karkare da babban taro ranar 14 ga wata, kuma za su cigaba da wannan shiri ba fashi.

Babban jigon hadakar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce su na son lallai INEC ta yi adalci.

Ita ma shugabar mata ta jam’iyyar Na’omi Abel ta ce akwai kalubale ga hanyar da ta ce an dauka ta maida Najeriya kasa mai bin jam’iyya daya.

In za a tuna shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ba ta sha’awar maida Najeriya kasa mai bin jam’iyyar daya.

A babban taron jam’iyyarsa ta APC, shugaba Tinubu ya ce ya yi amanna da tsarin gasa a harkokin dimokradiyya.

Za a zuba ido kan kotu da hukumar zabe don ganin ko akwai sauyin da za a iya samu yayin da kulle-kulle ko rashin jituwa ya jefa sufana a tayar ADC.

Wannan ba ma abun mamaki ba ne, don APC ma ta sha da kyar kan hatta sunanta gabanin zaben 2015 zamanin mulkin tsohon shugaba Jonathan da tsohon shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega.

 

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/ADC-VOWS-TO-GO-AHEAD-WITH-CONGRESSES-CALL-ON-AMUPITANS-SACK.mp3

 

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe
Next Post: Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz Wasanni
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
  • Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5 Labarai
  • Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu Afrika
  • CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
  • Babban Bankin Najeriya Ya Rage Kudin Ruwa Da Kashi Daya Cikin Dari Labarai
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
  • Ganduje: Mun Janye Shirin Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.