Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH
Published: April 25, 2026 at 4:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta hannun Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN), ta kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (Solar) mai karfin megawatt biyu (2MW) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) da ke Wudil a Jihar Kano.

Wannan aiki, wanda kudinsa ya kai naira biliyan 3.8, yana karkashin shirin nan na ‘Renewed Hope Solarization’ na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Baya ga aikin samar da wutar, an kuma kaddamar da fitilun kan hanya guda 200 masu amfani da hasken rana a cikin harabar jami’ar.

Darakta Janar na hukumar, Dr. Mustapha Abdullahi, tare da Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ne suka kaddamar da fara aikin a ranar Juma’a.

Dr. Abdullahi ya bayyana cewa an ba kamfanin da zai gudanar da aikin wa’adin watanni uku kacal domin kammalawa. Ya ce an tsara wannan aiki ne domin kawo karshen matsalar tsadar wutar lantarki da jami’ar ke fuskanta, inda take biyan naira miliyan 22.4 a kowane wata.

“Wannan aiki na Wudil yana bin sahu ne bayan makamancinsa da muka kaddamar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano a watan Satumban 2025, inda ake sanya tsarin megawatt hudu (4MW), da kuma aikin da muka kaddamar a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) a makon jiya,” in ji Dr. Abdullahi.

Ya kara da cewa an ba kamfanin Safiatu Global Resources Limited kwangilar a kan kudi naira biliyan 3.8, kuma ba za a kara ko sisi a kan kudin ba, sannan dole ne su kammala a cikin lokaci.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa jami’ar tana da dalibai da ma’aikata sama da 24,000, kuma bukatar wutar da take da ita ta kai tsakanin megawatt 12.3 zuwa 16.4. Sai dai, wutar da take samu daga kamfanonin rarraba wuta ba ta taka kara ta karya ba, yayin da janaretocin da take amfani da su ba sa iya daukar nauyin bukatar jami’ar.

A nasa jawabin, Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ya ce wannan aiki mataki ne na raya kasa a karkashin manufofin gwamnatin Tinubu na bunkasa ilimi da kirkire-kirkire ta hanyar samar da ingantaccen makamashi.

Shi ma a nasa bangaren, Shugaban Jami’ar, Farfesa Musa Tukur-Yakasai, ya nuna jin dadinsa da wannan gagarumin tallafi, inda ya ce wannan mataki zai kara bunkasa harkar bincike da koyarwa a jami’ar.

Afrika, Kimiya, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru
Next Post: Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Raba Naira Miliyan 14 Ga Iyalen ‘Yan Jaridan Da Suka Rasu Najeriya
Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026 Afrika
Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Wata Mata Da cikin Bogi Na ƙwaya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
  • Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
  • Yanbindiga sun Kashe mutun guda tare da yin garkuwa da mutane kimanin 100 a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsohon Ma’aikacin VOA Saleh Shehu Ashaka Ya Rasu Afrika
  • Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.