Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato
Published: April 29, 2026 at 3:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A wani mataki na fitar da jihar Filato dake Najeriya daga kangin tashe-tashen hankula da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin jihar, inda ya ba su umarnin komawa gida su fuskanci juna da zuciya ɗaya domin samar da dawwamamen zaman lafiya.

Haka zalika, Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin kudi har Naira Biliyan biyu (N2bn) a matsayin tallafin gaggawa ga mutanen da harin ranar 29 ga watan Maris ya rutsa da su a unguwar Anguwan Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Yayin taron wanda aka kwashe sa’o’i uku ana tattaunawa a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da shugabanni a kowane mataki za su cire son zuciya, su rungumi juna domin kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi.

“Ba maganar biki muke yi a nan ba,” in ji Shugaban Kasan. “Muna nan ne domin mu faɗawa juna gaskiya. Idan ana amfani da matasa ana rura wutar gaba da kisan juna, ku shugabanni ya kamata ku fara bincikar kanku.”

Shugaban ya kuma kalubalanci tawagar, karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, da su koma su duba duk wasu rahotannin tsofaffin kwamitoci (White Papers) da aka taɓa yi kan rikicin jihar, su fito da hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da su.

Tawagar mai mutum 32 ta haɗa da tsofaffin gwamnonin jihar; Sanata Simon Lalong, Sanata Jonah Jang, Joshua Dariye da Sir Fidelis Tapgun. Sauran sun hada da Sarkin Wase, Mai Martaba Mohammed Haruna; Gbong Gwon Jos, Da Jacob Gyang Buba; Shugaban kungiyar CAN na jihar, da kuma wakilan matasan Musulmi da Kirista.

A nashi ɓangaren, Gwamna Mutfwang ya nuna farin cikinsa, inda ya bayyana cewa wannan ne karon farko da dukkan tsofaffin gwamnonin jihar suka zauna a daki guda domin tattauna makomar jihar. Ya bayyana cewa wannan wata sabuwar baraka ce ta hadin kai da za ta taimaka wajen maido da martabar “Gidan Zaman Lafiya da Shakatawa.”

Shima Mai Martaba Gbong Gwon Jos, Da Jacob Gyang Buba, ya jinjinawa Shugaban Kasan, ya kuma bukaci a tura karin jami’an tsaro da kuma sanya na’urorin CCTV a lungu da sako na birnin Jos. Haka zalika, ya roki Shugaban da ya taimaka wajen ganin ’yan gudun hijira (IDPs) sun koma gidajen iyaye da kakanninsu kafin damuna ta kankama.

Taron ya zo ne a matsayin cika alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi na zama da masu ruwa da tsaki na jihar bayan munanan kashe-kashen da aka yi a watan Maris, inda ya jaddada cewa ba za a zuba ido ana kisan mutane ba tare da an hukunta wadanda ke rura wutar rikicin ba.

Masana na ganin cewa wannan zama na Abuja zai iya zama silar kawo karshen shekaru da dama na gaba da jidali a jihar, muddin shugabannin suka yi amfani da wannan damar wajen girmama juna da adalci.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano
Next Post: Mohammed Abdullahi Abubakar Ya Sayi fom Don Tsayawa Takarar kujeran Gwamnan Bauchi A APC 2027

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil Afrika
Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya Labarai
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisun Najeriya Sun Amince Ta Karin Kasafin Kudi Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jami’ai A Mexico Sun Tabbatar Da Kashe Shugaban Masu Shan Ƙwaya Nemesio Oseguera Labarai
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.