Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Najeriya Da Maroko Sun Kulla Yarjejeniya
Published: May 11, 2026 at 5:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Najeriya Da Maroko Za Su Kulla Yarjejeniya a fannin makamashi, noma, da kuma harkokin cinikayya

Alaƙar diplomasiyya tsakanin kasashen Najeriya da Maroko ta kara nuna ƙarfafa, inda kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar karfafa dangantaka a fannonin makamashi, noma, da kuma harkokin cinikayya.

Wannan sanarwa ta fito ne bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Ojukwu, da takwaranta na kasar Maroko, Nasser Bourita.

Babban kashin bayan tattaunawar shi ne aikin ginin bututun iskar gas na Najeriya da Maroko (African Atlantic Gas Pipeline). Ministocin biyu sun bayyana wannan gagarumin aiki a matsayin “mai canza alkiblar tattalin arziki” wanda zai samar da tsaro a fannin makamashi da kuma dunkulewar yankin Afirka ta Yamma baki daya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta tabbatar da cewa tuni kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) da takwaransa na kasar Maroko (ONHYM) suka kammala binciken fasaha na aikin. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarki Mohammed VI za su sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin a rubuce kafin karshen rubu’i na hudu na wannan shekara.

Baya ga batun iskar gas, kasashen biyu sun tattauna hanyoyin hadin gwiwa wajen sarrafawa da rarraba takin zamani. Wannan mataki na da nufin tabbatar da wadatar abinci ba kawai a kasashen biyu ba, har ma da sauran sassan nahiyar Afirka.

Domin farfado da tsoffin yarjejeniyoyin da aka kulla tun zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2018, Najeriya na shirin karbar bakuncin taron hadin gwiwa na kasashen biyu (Bilateral Joint Commission) karo na biyu.

Haka zalika, ministocin sun jaddada bukatar sake kafa Majalisar Kasuwanci ta Najeriya da Maroko. Sun bayyana cewa yarjejeniyar cinikayya ta bai-daya ta nahiyar Afirka (AfCFTA) da kuma shirin kauce wa biyan haraji ninki biyu, za su bude sabbin kofofin bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi

Karin Labarai Masu Alaka

Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka
Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika
  • Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
  • Yanbindiga sun Kashe kimanin mutane 30 a yankin kayama ta Jihar kwaran Najeriya Najeriya
  • An Tsinto Gawarwakin ‘Yan gudun Hijira A Bakin Tekun Comoros Labarai
  • Take Hakkin Dan Adam Zai Haifar Da Juyin Juya Hali A Najeriya Najeriya
  • Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai Sauran Duniya
  • Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.