Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe
Published: August 2, 2026 at 7:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta jihar Gombe (GOSEMA) ta kammala horon ƙara wa juna sani na kwanaki uku ga mambobin Kwamitocin Kula da Agajin Gaggawa na Ƙananan Hukumomi (Local Emergency Management CommitteesvLEMCs), da nufin ƙarfafa shirye-shiryen tunkarar bala’o’i da inganta ayyukan ba da agajin gaggawa a faɗin jihar.

An gudanar da horon ne ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren GOSEMA, Alhaji Haruna Abdullahi Haruna (Bacoza), inda aka tsara shi zuwa matakai uku domin bai wa mambobin kwamitocin daga dukkan ƙananan hukumomi goma sha ɗaya damar halarta, bisa shiyyoyin Gombe ta Arewa, Gombe ta Tsakiya da Gombe ta Kudu.

A jawabin da ya gabatar a buɗe taron da kuma lokacin rufe shirin, Babban Sakataren GOSEMA ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa goyon baya da kyakkyawan yanayin aiki da ya samar wa hukumar, wanda ya ba ta damar gudanar da ayyukan kare rayuka da dukiyoyin al’umma yadda ya kamata.

Alhaji Haruna Bacoza ya bayyana cewa kowace ƙaramar hukuma a Najeriya tana da Kwamitin Kula da Agajin Gaggawa wanda Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma ke jagoranta tare da sauran mambobi.

Ya ce kwamitocin na da muhimmiyar rawa wajen gano haɗurran da ka iya afkuwa, wayar da kan jama’a da kuma haɗa kai da hukumomin agajin gaggawa wajen ɗaukar matakan kariya.

Ya buƙaci mahalarta taron su koma yankunansu su isar da ilimi da dabarun da suka samu ga sauran mambobin kwamitocinsu da al’ummominsu domin ƙarfafa shirin tunkarar bala’o’i, rage asarar rayuka da dukiyoyi da kuma gina al’ummomi masu juriya.

A tsawon kwanaki ukun horon, ƙwararru daga GOSEMA, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe da Ƙungiyar Red Cross ta Najeriya sun gabatar da muƙalu kan muhimman fannoni na kula da bala’o’i.

Daga cikin muƙalun akwai Tsarin Gargaɗin Farko na Bala’o’i a Matakin Al’umma, Taswirar Haɗurra a Matsayin Muhimmin Kayan Aikin Gudanar da Haɗarin Bala’o’i, Shirye-shiryen Tunkarar Bala’o’i da Tsare-tsaren Ba da Agajin Gaggawa, Hanyoyin Rage Haɗarin Gobara da Kare Kai a Matakin Al’umma, da kuma Gabatarwa ga Agajin Farko da Kula da Gaggawa.

Masu gabatar da darussan sun jaddada muhimmancin taswirar haɗurra, tsarin gargaɗin farko, shirye-shiryen tunkarar bala’o’i, saurin ba da agajin gaggawa, kariya daga gobara, ilimin agajin farko da haɗin kan al’umma wajen rage illolin bala’o’i.

Sun kuma yabawa sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da ƙungiyoyi masu zaman kansu bisa gudummawar da suke bayarwa wajen wayar da kai da hidimtawa al’umma.

Horon ya gudana cikin tattaunawa mai armashi, inda mahalarta daga dukkan ƙananan hukumomin jihar suka gabatar da tambayoyi, suka bayyana ƙalubalen da suke fuskanta a yankunansu tare da musayar ƙwarewa kan hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i.

GOSEMA ta bayyana cewa horon na daga cikin dabarun gwamnatin Jihar Gombe na gina ingantaccen tsarin gudanar da harkokin agajin gaggawa a matakin ƙasa da ƙasa, tare da tabbatar da cewa kowace al’umma ta samu ilimi da ƙwarewar da za su taimaka wajen rage haɗarin bala’o’i da kare rayuka da dukiyoyi.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya
Next Post: Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba

Karin Labarai Masu Alaka

Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika
Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
  • Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci Afrika
  • Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko Najeriya
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Game Da Matsalar Tsaro A Najeriya Najeriya
  • Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.