Shahararren ɗan wasan Kannywood kuma Darakta-Janar na National Film Corporation, Ali Nuhu, an nada shi a matsayin Mataimakin Darakta a kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Ali Nuhu na daga cikin fitattun mutane biyu daga masana’antar Kannywood da aka nada a mukamai daban-daban a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen.
Ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a, da kuma neman ƙuri’u da goyon baya ga Shugaba Tinubu, musamman tsakanin ‘yan fim, masu shirya fina-finai da sauran ƙwararru a masana’antar nishaɗi.
Nadin nasa na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen ƙasar da ake sa ran gudanarwa a shekarar 2027.


