Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

UEFA Tana Shirin Janye Barazanar Kauracewa Gasar FIFA
Published: August 26, 2026 at 8:31 PM | By: Bala Hassan

UEFA Ta Shirin Janye Barazanar Kauracewa Gasar FIFA Yayin Da Italiya Ta Janye Goyon Bayanta Ga Infantino

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai, UEFA, na shirin janye barazanar da ta yi na kauracewa gasannin FIFA, bayan ta samu tabbacin cewa ba za a sake farfado da shirin sayar da kaso na gasannin Kofin Duniya da sauran manyan gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu ba.

Rahotanni sun ce UEFA ta samu wannan tabbaci ne yayin da Italiya ta zama sabuwar hukumar kwallon kafa ta kasa da ta janye goyon bayanta ga Shugaban FIFA, Gianni Infantino, a zaben shugaban hukumar da za a gudanar a watan Maris na shekara mai zuwa.

Hukumar Kwallon Kafa ta Italiya (FIGC) ta ce matakin nata na janye goyon bayan Infantino ya kasance ne domin bayyana matsayinta karara kan wasu sabbin matakan da shugaban FIFA ya dauka game da tafiyar da harkokin kwallon kafa da kuma ci gaban manyan gasannin kasa da kasa.

Matakin na UEFA ya samo asali ne daga wani shirin FIFA da ya tayar da kura a watan Yuli, wanda ya kunshi kafa wata sabuwar hukuma ta kasuwanci da kuma sayar da kaso 20 cikin 100 na hakkokin kasuwancin wasu manyan gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu.

Shirin ya fuskanci adawa daga dukkanin kungiyoyin kwallon kafa 55 da ke karkashin UEFA, wadanda suka amince da yiwuwar kauracewa gasannin FIFA idan aka ci gaba da shirin.

Sai dai yanzu, majiyoyin da ke sane da tattaunawar sun ce jami’an UEFA za su sanar da kwamitin zartarwa da shugabannin mafi yawan kungiyoyin kasashe mambobin ta cewa an cika sharuddan da suka kafa domin janye barazanar kauracewar.

UEFA ta bukaci abubuwa biyu: a janye shirin gaba daya, sannan a ba ta tabbacin cewa ba za a sake gabatar da irin wannan shiri a nan gaba ba.

Wata majiya da ke sane da tattaunawar ta ce matakin ba nasara ko rashin nasara ba ne ga UEFA, sai dai hanya ce ta kauce wa cutar da matasan ‘yan wasa da damar da suke samu na shiga manyan gasannin kasa da kasa.

A gefe guda kuma, matsin lamba na ci gaba da karuwa kan Infantino, yayin da UEFA, hukumar kwallon kafa ta Asiya (AFC) da CONCACAF ke tattauna yiwuwar kada kuri’ar rashin amincewa da shi gabanin zaben shugaban FIFA na watan Maris.

Infantino, wanda ke neman wa’adi na hudu a matsayin shugaban FIFA, har yanzu yana da goyon bayan kungiyoyin kwallon kafa na Afirka da Kudancin Amurka.

Sai dai wasu manyan jami’an kwallon kafa na Turai sun bayyana cewa makomar Infantino a FIFA na cikin hadari, yayin da ake kara samun kiraye-kirayen neman sauya tsarin tafiyar da hukumar.

Duk da rikicin, FIFA ta tabbatar da cewa dukkan kasashen da suka samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 20 da za a gudanar a Poland za su halarta, lamarin da ya rage fargabar cewa rikicin zai shafi gasannin FIFA nan take.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Feyenoord Ta Fara Tattaunawa Da Manchester United Kan Daukar Chido Obi Aro 

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amy Hunt Ta Zama Sabuwar Tauraruwar Wasannin Guje-guje Ta Birtaniya Wasanni
FIFA Ta Buɗe Bincike Kan Koci Hossam Hassan Na Masar Wasanni
Arsenal Ta Fara Kare Kambun Gasar Premier League Da Ci 3-0 A Kan Coventry City Wasanni
‘Yan Sanda Sun Kama Mutane Takwas Da Ake Zargi Da Siyar Da Tikitin AFCON Ba Bisa Ka’ida Ba Wasanni
AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • UEFA Tana Shirin Janye Barazanar Kauracewa Gasar FIFA
  • Feyenoord Ta Fara Tattaunawa Da Manchester United Kan Daukar Chido Obi Aro 
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Afrika
  • Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya
  • Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
  • Netanyahu Yana Neman Shawarwari Daga Hukumomin Lebanon Labarai
  • Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe Labarai
  • An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.