Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha Afrika
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8 Afrika
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam Afrika

Manoma Da Makiyaya: An Bukaci A Gaggauta Tantance Hanyoyin Shanu Da Iyakoki A Dukku
Published: August 30, 2026 at 10:42 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Karamar Hukumar Dukku ta jihar Gombe, Honarabul Abubakar Adamu, ya shirya taron tattaunawa da shugabannin gargajiya, manoma, makiyaya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke kunno kai a yankin.

An gudanar da taron ne a fadar Hakimin Bozonsulwa da ke Waziri ta Kudu, inda aka mai da hankali kan samar da mafita mai dorewa ga matsalolin da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro, musamman rashin fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar Dukku, Honarabul Abubakar Adamu, ya ce ya gayyaci jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalolin da ake fuskanta tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen dakile rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

A nasa jawabin maraba, Hakimin Bozonsulwa, Alhaji Kamalu Hayatu Gurama, ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Dukku da jami’an tsaro bisa shirya taron wayar da kan manoma da makiyaya kan muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna.

Ya ce irin wannan tattaunawa na da muhimmanci wajen rage rashin fahimtar juna da kuma hana ayyukan da ka iya haifar da tashin hankali tsakanin al’ummomin yankin.

Shi ma Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na jihar Gombe, Dakta Ardo Chindo Abubakar, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, manoma, makiyaya da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen wayar da kan matasa game da muhimmancin zaman lafiya da zaman tare.

Dakta Chindo Abubakar ya tabbatar da cewa kwamitinsa zai ci gaba da hada kai da hukumomin da abin ya shafa wajen tantancewa da kafa iyakokin hanyoyin da shanu ke bi, tare da tabbatar da bin hanyoyin kiwo da aka amince da su, domin dakile rikice-rikice a fadin jihar.

A jawabansu daban-daban, Jami’in ’Yan Sandan da ke kula da Sashen ’Yan Sanda na Dukku, ASP Nura Sulaiman, da wakilan sauran hukumomin tsaro, sun bukaci manoma da makiyaya da su rungumi tattaunawa a matsayin hanya mafi dacewa wajen warware sabanin da ke tsakaninsu, maimakon daukar mataki da zai iya haifar da rikici.

Jami’an tsaron sun kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a yankin da su wayar da kan al’ummominsu kan muhimmancin kiyaye zaman lafiya da tsaro.

A jawabinsa na karshe, Shugaban Karamar Hukumar Dukku, Honarabul Abubakar Adamu, ya gode wa Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa kokarinsa na samar da ci gaba, musamman ayyukan da ake gudanarwa a Wawa-Zange Grazing Reserve.

Ya kuma yi kira ga matasan Fulani da su guji daukar doka a hannunsu, tare da yin gargadi kan kutsawa cikin gonakin manoma ta hanyar kai dabbobi cikin gonaki.

Shugaban ya kuma bukaci Kwamitin aiwatar da yarjejeniyar tsakanin manoma da makiyaya da ya ci gaba da tantancewa da sanya alamar iyakokin hanyoyin shanu da wuraren kiwo a cikin Karamar Hukumar Dukku, domin hana rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin manoma da makiyaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Zulum Ya Jinjinawa Hadiza Aliyu Kan Naɗin Ta A Matsayin Babbar Editar NAN
Next Post: Shugaba Tinubu Zai Shafe Makonni Uku A Hutun Shekara-Shekara

Karin Labarai Masu Alaka

Matatar Man Dangote Zata Wadatar Da Najeriya Da Makota Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
Bola Ahmed Tinubu Ya Soke Bashin Da Gwamnati Take Bin NNPC Najeriya
An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi
  • Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH
  • Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Kama Dattijo Kan Zargin Cin Zarafin Yarinya ’Yar Shekara 8
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jami’ai A Afirka Sunce Tashin Farashin Mai Kalubale Ne Ga Tattalin Arziki Afrika
  • Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
  • Kaduna: Masana Sun Nemi A Sauya Tsohon Wurin Zubar Da Shara Na Tudun-Ilu Afrika
  • Sabon Jadawalin Gasar Kwalon Kafa Ta Turai 2026 Wasanni
  • Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
  • Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
  • Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.