Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro Afrika
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN Afrika
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira Afrika
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe Afrika
  • An Horar Da Mata Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Gombe Afrika

Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
Published: September 6, 2026 at 4:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: September 6, 2026

Majalisar Malaman Yarbawa a Gombe, wato Yoruba Council of Ulama Gombe Nigeria, YCUGN, ta bayyana alhini da jimami bisa rasuwar Babban Limamin Ƙungiyar Nuruddeen Society of Nigeria, reshen Jihar Gombe.

A cikin saƙon ta’aziyyar da Babban Sakataren majalisar, Sheikh Alfa Okegbemiro Jamiu Okesola, ya sanya wa hannu a ranar 6 ga Satumba, 2026, majalisar ta bayyana marigayin a matsayin uba, malamin addini, shugaba kuma mai koyarwa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautar Allah, yada ilimin addinin Musulunci da kuma haɗa kan al’umma.

Majalisar ta ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan Musulmi, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimin Alƙur’ani da sauran harkokin addini a Jihar Gombe.

A cewar sanarwar, shugabancinsa ya kasance bisa tawali’u, hidima da hikima, inda ya yi amfani da matsayinsa wajen sasanta rikice-rikice, bayar da shawarwari da kuma jagorantar al’umma bisa koyarwar Musulunci.

Majalisar ta kuma bayyana marigayin a matsayin mutum mai karamci da kishin al’umma, musamman talakawa, marayu da ɗaliban ilimin addini.

Ta ce gudunmawar da ya bayar wajen tallafa wa makarantun Islamiyya, masallatai da iyalai a Gombe na daga cikin abubuwan da za su ci gaba da kasancewa cikin tarihin rayuwarsa.

Majalisar Malaman Yarabawa ta yi kira ga mambobin Ƙungiyar Nuruddeen da sauran Musulmi da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’un da marigayin ya kasance yana koyarwa, musamman haɗin kai, gaskiya, haƙuri, tawali’u da hidima ga al’umma.

Ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da tallafa wa karatun Alƙur’ani da sauran ayyukan da ke inganta rayuwar al’umma da haɗin kan Musulmi.

Majalisar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa, Ya yalwata masa kabarinsa tare da sanya haske a cikinsa, sannan Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.

Haka kuma, majalisar ta roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin, Ƙungiyar Nuruddeen, al’ummar Yarabawa da ɗaukacin Musulmin Jihar Gombe haƙurin jure wannan babban rashi.

Ta ƙara jaddada buƙatar ci gaba da ayyukan alheri da ilimi da marigayin ya bari, domin su zama abin tunawa da kuma ci gaba da amfanar al’umma.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba
Next Post: Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon Afrika
Yanayin Yunwa Yana Kara Ta’azarra A Somaliya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe
  • Tinubu Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Sake Zaɓensa A 2027

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
  • Lauyoyi Sun Gurfanar Da Wani A Kotu Bisa Fasa Korin Kiyashi A Kenya Afrika
  • Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
  • Wasu Lauyoyi Sunyi Murabus Yayin Gudanar Da Wata Shari’a A Kasar Amurka Amurka
  • Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
  • Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Ta Tabbatar Da Kyautata Rayuwar Mambobin ta Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.