Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Gwamna Buni Ya Gana Da Limamai, Ya Buƙaci Su Taimaka Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya
Published: October 19, 2026 at 10:27 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Yobe a Najeriya Mai Mala Buni, ya buƙaci manyan limaman masallatan Juma’a da ke Damaturu, babban birnin jihar, da su ƙara himma wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Jihar Yobe da Najeriya baki ɗaya.

Gwamna Buni ya yi wannan kira ne a lokacin da ya gana da limaman, inda ya buƙace su da su riƙa isar da saƙonnin soyayya, zaman lafiya, haƙuri da fahimtar juna a cikin huɗubobin sallolin Juma’a.

Gwamnan ya tunatar da limaman irin munanan abubuwan da jihar ta fuskanta a baya, yana mai jaddada cewa Jihar Yobe ba za ta iya ɗaukar wani sabon rikici ba.

Ya kuma bayyana muhimmancin ƙara yawaita addu’o’i da wayar da kan al’umma kan buƙatar zaman lafiya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe mai zuwa.

Gwamna Buni ya buƙaci limaman da su yi amfani da matsayinsu wajen ƙarfafa wa al’umma gwiwar rungumar zaman lafiya da kauce wa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga tsaro da haɗin kan jihar.

Tun da farko, Mai Bai wa Gwamnan Shawara kan Harkokin Addini, wanda kuma shi ne mai shirya taron, Ustaz Babagana Malam Kyari, ya yaba wa Gwamna Buni bisa matakan da yake ɗauka tun da wuri domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin yaƙin neman zaɓe a jihar.

Ustaz Babagana ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa wannan kira na gwamnan zai ƙara zaburar da limaman wajen yawaita addu’o’i da tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da zaɓe cikin lumana da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Taron na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na haɗa kai da shugabannin addini domin inganta zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar Yobe.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Rundunar ’Yan Sandan Bauchi Ta Yi Gargaɗi Kan Ɗaukar Doka A Hannu Bayan Kama Mutum 17
Next Post: Gombe: NEDC Za Ta Samar Da Motocin Lantarki Domin Rage Tsadar Kuɗin Sufuri

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf Afrika
Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci Afrika
ACReSAL Ta Tallafa Wa FMC Kumo, Ta Shuka Bishiyoyi Tare Da Gyara Magudanan Ruwa Afrika
Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika
  • Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto Najeriya
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.