Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da kokarin gina kasa mai wadata, tare da karfafa tattalin arziki, zuba jari a makomar matasa da kuma aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake tsokaci kan ziyarar ibadar Umara da ya kai kasar Saudiyya, inda ya samu damar shiga cikin dakin Ka’aba mai alfarma da ke birnin Makkah domin gudanar da addu’a.
Tinubu ya nuna godiyarsa ga Mai Kula da Harami Biyu Masu Alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba shi da sauran tawagarsa ta Najeriya na shiga cikin Ka’aba domin yin addu’a.
Ya bayyana wannan dama a matsayin wata babbar karamci mai tarihi da ba zai taba mantawa da ita ba, yana mai cewa hakan na kara tabbatar da kyakkyawar dangantaka, zumunci da hadin kai tsakanin Najeriya da Saudiyya.
Shugaban ya ce ya yi amfani da wannan dama wajen rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi hikima da juriyar da za su taimaka masa wajen ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima yadda ya kamata.
A cewarsa, damar jagorantar Najeriya a matsayin Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin kasar wata babbar ni’ima ce daga Allah, wadda wajibi ne ya rama ta ta hanyar jajircewa wajen yi wa kasa hidima.
Haka kuma, Tinubu ya yi tsokaci kan sakon da ke cikin Alkur’ani mai girma, musamman Suratu Ali Imran, aya ta 26, wadda ta bayyana cewa Allah Madaukakin Sarki ne mamallakin mulki da iko, Yana ba wa wanda Ya so mulki, kuma Yana karbe shi daga wanda Ya so.
Ya jaddada cewa wannan koyarwa na nuna cewa dole ne shugabanni su gudanar da mulki cikin tawali’u, amana da kuma kishin al’ummar da suke jagoranta.
Shugaban ya kara da cewa aniyarsa ta gina Najeriya, wadda ya kira Project Nigeria, ta kara karfi, yana mai tabbatar da kudurinsa na ganin kasar ta samu ci gaba da wadata bisa yardar Allah da kuma bukatun al’ummar kasar.
Dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, Tinubu ya bayyana kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa an gina tubali mai karfi, kuma kasar na samun ci gaba bayan tsallake wani mawuyacin yanayi na tattalin arziki.
Ya kuma jaddada muhimmancin zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabannin yau suka dauka za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance irin tarihin da al’ummomi masu zuwa za su tuna da su.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen karfafa tattalin arziki, samar da damarmaki ga matasa da kuma gina yanayin da zai bai wa ‘yan Najeriya damar cimma burinsu.
A wani bangare kuma, Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Al’umma, Ali Pate, tare da gwamnonin jihohin Borno, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Yobe da Kwara, da wasu manyan ‘yan kasuwa, sun nuna godiyarsu ga Allah bisa damar da suka samu na shiga cikin Ka’aba tare da gudanar da addu’a.
Daga cikin ‘yan kasuwar akwai Shugaban Kamfanin BUA Group, Abdulsamad Rabiu, da Babban Jami’in Kamfanin Oando, Wale Tinubu.
Wannan bayani na Shugaban Kasa na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin.


