Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi
Published: March 23, 2026 at 10:26 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ana sa ran farashin mai zai ƙara tashi a yau Litinin, bayan da ya rufe kasuwa kafin ƙarshen mako a mafi girman matsayinsa cikin kusan shekaru huɗu, sakamakon barazanar da Amurka da Iran suka yi na kai hari kan cibiyoyin makamashi, a cewar manazarta a jiya Lahadi.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar a ranar Asabar cewa zai “lalata gaba ɗaya” tashoshin wutar lantarki na Iran idan Tehran ba ta sake buɗe mashigar ruwan Hormuz gaba ɗaya cikin sa’o’i 48 ba. Wannan na nuna ƙarin tsanani a rikicin, kasa da kwana guda bayan ya yi maganar “rage zafin yaƙin,” wanda yanzu ya shiga mako na huɗu.

A nata ɓangaren, Iran ta yi gargaɗi a ranar Lahadi cewa za ta kai hari kan muhimman ababen more rayuwa da ke da alaƙa da Amurka, ciki har da cibiyoyin makamashi da na sarrafa ruwan teku zuwa ruwan sha a yankin Tekun Fasha, idan Trump ya aiwatar da barazanar tasa.

A ranar Juma’a, kasuwar Man Brent na watan Mayu sun rufe da ƙarin kashi 3.26 cikin ɗari, zuwa dala 112.19 kan kowace ganga, wanda shi ne mafi girma tun watan Yuli na shekarar 2022.

“Barazanar da Shugaba Trump ya yi yanzu ta sanya kasuwanni cikin wani yanayi na rashin tabbas mai tsanani na tsawon sa’o’i 48,” in ji Tony Sycamore, manazarcin kasuwa na kamfanin IG. Ya ƙara da cewa idan ba a janye wannan wa’adin ba, farashin mai zai yi tashin gwauron zabo a ranar Litinin.

Afrika, Amurka, Labarai, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC
Next Post: Ana Kokarin Dawo Da Wutan Lantarki A Cuba

Karin Labarai Masu Alaka

Sudan Takai Hari Kasar Chadi Da Jirgi Marar Matuki Afrika
Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
Ansamu Maganin Da Yake Rage Kitsen Jijiyoyi A Amurka Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojoji Zasu Taimakawa ‘Yan Sanda Wajen Yaki Da Mugayen Ayyuka Labarai
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
  • Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
  • Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.