Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe
Published: February 1, 2026 at 1:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 1, 2026

An Kaddamar da Kwamitin Gasar Kofin Haɗin Kan Masarautun Gargajiya na Gombe 2026

An kaddamar da Kwamitin Shirya Gasar Ƙwallon Ƙafa ta Haɗin Kan Masarautun Gargajiya na jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya, wadda aka fi sani da Kofin Haɗin Kan Sarkin Gombe 2026, a hukumance a birnin Gombe.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a taron farko na kwamitin, inda aka miƙa wa mambobinsa takardun shaidar aikinsu. Bayan haka, an gudanar da taron manema labarai da ya samu halartar wakilan manyan kafafen yaɗa labarai.

Da yake jawabi yayin taron, Shugaban Kwamitin kuma mai ɗaukar nauyin gasar, Ahmed Shuaibu Gara Gombe, ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da kuma bunƙasa matasa ta hanyar wasanni a masarautun gargajiya na jihar.

Ya ƙara da cewa gasar za ta gudana ne da tsarin haɗaka, inda za a raba ƙungiyoyin da za su fafata gida huɗu a cibiyoyi huɗu, bisa shawarwarin da Kwamitin Fasaha zai bayar.

Ahmed Shuaibu Gara Gombe ya kuma sanar da kyaututtuka masu tsoka da aka tanada kuma kungiyar da ta zama zakara za ta samu naira miliyan biyar tare da kofi, ta biyu kuma naira miliyan uku, yayin da ta uku za ta samu naira miliyan biyu.

Haka kuma za a bayar da lambobin yabo na musamman ga Mafi Kyawun Mai Tsaron Raga, Wanda Ya Fi Zura Ƙwallaye, Fitaccen Ɗan Wasa na Gasar, da kuma Ƙungiyar da Ta Fi Nuna Wasan Gaskiya, duk tare da kofuna.

Mai ɗaukar nauyin gasar ya kuma bayyana cewa za a fara rangadin nuna kofin gasar a faɗin jihar daga Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026, zuwa Jumma’a, 6 ga Fabrairu, 2026.

Rangadin zai zagaya dukkan masarautun gargajiya 15 na jihar, farawa daga Masarautun Nafada da Funakaye, sannan ya wuce Yamaltu, Deba, Waja, Kaltungo, Tangale, Akko, Pindiga, Cham, Dadiya, Tula, Gona, da Dukku.

Ana shirya gasar Kofin Sarkin Gombe ta 2026 ne tare da ɗaukar nauyinta daga kamfanin Green White Green Sports Center Limited, tare da goyon bayan Mai Martaba Sarkin Gombe.

Ana sa ran gasar za ta ƙara bunƙasa harkokin ƙwallon ƙafa a matakin tushe tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummomin jihar Gombe.

Kwamitin shirya gasar na ƙarƙashin jagorancin Ahmed Shuaibu Gara Gombe a matsayin Shugaba, yayin da Auwal Musa Umar, tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta jihar Gombe, ke matsayin Mataimakin Shugaba.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da masu riƙe da sarautun gargajiya da wakilan al’umma, yayin da Haruna Abdullahi yake a matsayin Sakatare da Yakubu Maikudi Jami’an yada labarai tare da masu kula da harkokin yaɗa labarai da tallafin tsare-tsare na Musamman.

Labarai, Najeriya, Wasanni

Post navigation

Previous Post: Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga
Next Post: Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Duk Da Rauni Daya Samu Sakamakon Hari Mojtaba Khameni Yafara Aiki Labarai
Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallar Azumi Afrika
Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna Amurka
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka
  • CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
  • Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jami’an tsaro sama da dubu biyar ne zasuyi aikin tabbatar da tsaro Alokacin bikin karamar sallah a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.