Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato
Published: March 25, 2026 at 7:21 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Matsalolin tsaro dake da fuskoki daban-daban da suka addabi al’ummar jihar Filato na dab da kawo karshe, bayan hukumomi sun fara gano wadanda ke warware kokarin zaman lafiya a jihar.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ne ya bayyana hakan, yayinda al’ummar musulmin jihar Filato suka kai masa gaisuwar Sallah a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang wanda ya yaba da ziyarar na hada dankon zumunci a tsakanin gwamnati da al’umma, ya kuma ce sun fara fahimtar wadanda ke hana samun zaman lafiya kuma suna daukar matakai.

Alhaji Garba Abdulkadir, shine mataimakin shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam a jihar Filato, yace manufar zuwansu shine don fatan Samun alkhairi.

Shima Alhaji Sani Mu’azu, Makaman Jos ta Arewa, yace al’ummar musulmi sun yi godiya ne saboda an gudanar da Sallah lafiya.

Mamba mai wakiltar shiyyar Jos ta Arewa maso Arewa, a majalisar dokokin jihar Filato, Adamu Aliyu yace suna bawa hukumomi shawarwari kan daukan matakan tsaro.

Al’ummar musulmin sun kuma mika wa gwamnan huhun goro, yayinda shima gwamnan na jihar Filato, Caleb Mutfwang ya mika musu nashi goron don nuna hadin kai da amincewa da juna,

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AUD-20260325-WA0003.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Tsofin Ma’aikatan Gwamnati Sunyi Zanga Zanga A Jihar Neja
Next Post: Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila

Karin Labarai Masu Alaka

Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ronaldo Da Messi Ka Iya Hadu A Gasar Cin Kofin Duniya: Ta Ya Ya ? Wasanni
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
  • Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
  • Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
  • Iran Zata Sassauta Shirin Nukiliya Tsakaninta Da Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe Najeriya
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.