Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya
Published: March 16, 2026 at 8:37 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yanzu yaki tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya shiga mako na uku, ba tare da wata alama karara ta tsagaita shi ba, abinda yayi sanadiyyar rufe mashigin ruwa na Hormuz, inda ta nan ne ake jigilar Kashi 20 cikin 100 na man fetur da gas na duniya. Wannan yasa farashin man fetur da sauran makamashi ya tashi, kuma ana fargaban hakan Zai iya jawo hauhawar farashin kayayyaki a duk fadin duniya.

Isra’ila tace a ranar Litinin ta yi tsararren shiri na ci gaba da fafata yaki har zuwa nan da mako uku, yayin da take ci gaba da kaiwa Iran hari. Ita kuma Iran ta kai hari da jirage marasa matuki na drone da ya sa aka rufe filin jirgin sama na Dubai na wani dan lokaci, sannan kuma harin ya shafi wata babbar cibiyar man fetur a Hadaddiyar Daular Larabawa.

A ranar Lahadi, shugaban Amurka, Donald Trump yayi kira ga kasashe su kawo dauki don a bude mashigin ruwa na Hormuz, kuma yace kungiyar NATO nan gaba zata fuskanci mummunan yanayi, idan bata taimaka ba. Amma ‘yan kawancen Amurka suna so a bi hanyar diplomasiyya wajen bude mashigin ruwan, suna dari darin shiga yaki.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato
Next Post: Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
Trump Yace Amurka Ta Kai Hare-Hare Masu Yawa Akan ‘Yan Ta’adda A Najeriya Amurka
Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
  • Tinubu Yafara Wasu Dabaru Domin Samun Kuri’u Siyasa
  • Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
  • Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
  • Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
  • Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.