Farashin mai yayi tashin gwaron zabi ranar jumma’a, ya kai kudi da rabon da aga haka kusan shekaru hudu da suka wuce a yayinda Iraqi ta ayyana abunda kusan za’a kira dokar ta baci, ta gayawa abokan cinikayyarta cewa ba zata iya cika alkawari ba, ganin galibin man kasar duka ta mashigin ruwan Hormuz ake fitar da shi, a kuma dai dai lokacin da Amurka take shirin tura karin dubban dakaru zuwa yankin.
Mai mafi daraja da ake kira Brent ana cinikinsa kan dala 112 d centi 19 kan ko wace ganga, farashi mfi tsada rabon da a yi cinikin mai kan haka tun cikin watan Yuli na shekara ta 2022, yayinda mai da ake kira West Texas ya tsaya kan dala 98 da centi 32 kan ko wace gangar danyen mai.
A gefe daya kuma, shugaban hukumar makamashi, wanda har wa yau shine ministan wannan sashe a Qatar, yace yayi gargadin cewa kasar zata fuskanci matsalar data fada ciki na hari daga Iran kan cibiyoyin makamashinta, muddin aka kaiwa Iran hari kan cibiyoyin makamashinta.


