Gwamnan jihar Sokoto, a Najeriya Dr. Ahmad Aliyu Sokoto, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 wanda ya haura Naira biliyan 700, inda ya bayyana kudurin gwamnatinsa na ƙarfafa harkokin kiwon lafiya da ilimi a jihar.

Yayin gabatar da kasafin kuɗin ranar laraba, Dr. Ahmad Aliyu Sokoto ya bayyana cewa gwamnati za ta ware muhimman kuɗaɗe domin kammala Wasu Ayukka da yagada daga gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal daga ciki akwai Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Sokoto da kuma manyan Asibitoci uku dake sabon birni da Binji da Tambuwal da kuma Asibitin Murtala da akafara tun lokacin mulkin Yahaya AbdulKarim.
Yadai mika kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, inda ake sa ran ‘yan majalisar za su fara nazari da tattaunawa a kai nan gaba kadan.
Idan aka amince da kasafin, za’a soma aiwatar da shi ne a watan Janairu na shekarar 2026.


