Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
Published: July 1, 2026 at 5:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: July 1, 2026

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da aikin gina babbar hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Biu–Maiduguri, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce zai inganta hanyoyin sufuri da bunƙasa tattalin arziki a sassan Arewacin Najeriya.

An gudanar da bikin ƙaddamar da aikin ne a garin Akwanga na jihar Nasarawa, inda Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya wakilci Shugaba Tinubu.

A cewar gwamnatin tarayya, aikin na daga cikin manyan ayyukan da ake aiwatarwa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, domin haɗa yankunan tekun Najeriya, savanna da yankin Sahel ta hanyar ingantacciyar hanyar mota, da nufin ƙarfafa kasuwanci, sauƙaƙa zirga-zirga da haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Yilwatda ya ce aikin ya nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za su haifar da ci gaban tattalin arziki, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma inganta rayuwar al’ummar Najeriya.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yabawa Shugaba Tinubu kan ba da fifiko ga ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa.
Ya ce idan aka kammala aikin, zai haɓaka kasuwanci, rage lokacin tafiya, inganta tsaro, samar da guraben aikin yi tare da haɗa al’ummomi da kasuwanni a sassa daban-daban na ƙasar.

Shi ma Gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang, ya ce al’ummar Arewacin Najeriya na yaba da yadda gwamnatin tarayya ke rabon ayyukan ci gaba cikin adalci, yana mai bayyana babbar hanyar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za su kasance abin tunawa a gwamnatin Shugaba Tinubu.

A nasa ɓangaren, Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya bayyana cewa za a aiwatar da aikin ne bisa ƙa’idojin aikin injiniya na zamani ta hannun ƙwararrun kamfanoni, yana mai cewa hakan zai inganta harkokin sufuri, rage kuɗin jigilar kayayyaki da kuma buɗe sabbin damammakin tattalin arziki ga yankunan da hanyar za ta ratsa.

Tun da farko a ranar, Gwamna Inuwa Yahaya ya halarci ƙaddamar da gadar ƙasa (Underpass) mai tsawon mita 600 da kuma sabbin hanyoyin cikin garin Akwanga, inda ya taya Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, murnar kammala ayyukan tare da yabawa gwamnatinsa bisa ƙoƙarin bunƙasa ababen more rayuwa.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin akwai Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Jamilu Isyaku Gwamna ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa na APC, Sanata Ahmad Aliyu Wadada da kuma sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da sauran manyan baƙi daga jihohin Gombe, Nasarawa da Plateau.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed
Next Post: Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa

Karin Labarai Masu Alaka

Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi Afrika
Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo Afrika
“Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
  • An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin Afrika
  • Shugaban Kasar Ukraine Yace Rasha Tana Bawa Iran Bayanan Sirri Afrika
  • Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
  • An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
  • China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.