Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar
Published: February 5, 2026 at 10:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi Allah wadai da ƙaruwar hare-hare da kashe kashen da ake yi kwanan nan a sassan jihohin Kwara, Katsina da Benue, yana mai bayyana su a matsayin abin takaici, rashin hankali kuma cin zarafi kai tsaye ga al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Wannan Allah wadai ya biyo bayan hare-haren da aka kai a ƙauyukan Woro da Nuku ne a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta jihar Kwara, inda ake zargin ‘yan ta’adda sun kai hari a daren Talata da kisan aƙalla mutane 20 a ƙauyen Doma A da Doma B na Gundumar Tafoki, a Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina da kuma wani lamari na daban a ƙauyen Abande na gundumar Mbaikyor da Turan, a Ƙaramar Hukumar Kwande ta jihar Benue, inda aka ruwaito cewa an kashe mutane da dama.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar bakin ciki game da waɗánnan mummunan asarar rayuka na waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da al’ummomin da abin ya shafa da kuma gwamnatoci da al’ummomin jihohin uku.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yabawa Gwamnonin jihohin Kwara, Katsina da Benue bisa jagoranci da jajircewarsu a duk lokacin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro da ake yawan fuskanta, yana mai bayyana ƙoƙarinsu na tallafawa al’ummomin da abin ya shafa, da ƙarfafa tsarin tsaro a yankin da kuma haɗa kai da hukumomin tarayya don farfaɗo da zaman lafiya.

Ya yi ƙira ga hukumomin tsaron ƙasar su ƙara himma wajen tattara bayanan sirri, da sanya ido da kuma ɗaukar matakan da suka dace na gano waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma waɗanda ke tallafa musu, yana mai jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi babban alhakin ne dake kan duk wani shugaba.

“Ƙungiyar Gwamnonin Arewa tana goyon bayan hukumomin tsaronmu kuma tana ƙira a garesu, su ɗauki duk wani matakin daya dace don gurfanar da masu laifin a gaban shari’a. Bai kamata masu aikata waɗannan laifukan su sha ba tare da hukunci ba,” in ji Gwamna Inuwa Yahaya.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin na Arewa ya tabbatarwa ‘yan Najeriya jajircewar Ƙungiyar ta yi na yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya, da hukumomin tsaro, da masarautun gargajiya da shugabannin al’umma don magance matsalolin rashin tsaro ta hanyar haɗakar matakan tsaro masu ƙarfi, da tattara bayanan sirri da leƙen asiri da kuma samar da tallafi a harkokin tattalin arziƙi da zamantakewa na dogon lokaci.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka mutu, sannan ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya baiwa waɗanda suka ji rauni sauƙi, yayin da ya yi ƙira ga ‘yan ƙasar da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da yin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro don daƙile aika-aikar ta’addanci.

Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Al’ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta sharewa gidaje sun Koka.
Next Post: Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka

Karin Labarai Masu Alaka

Kakakin Majalisar Kasar Amurka Yana Tsaka Mai Wuya Game Da Kasafin Kudi Amurka
Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
Rasha Ta Gargadi Amurka Da Isra’ila Kan Harin Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hare Hare A Kasar Congo Ya Jikkata Mutane Da Dama Afrika
  • Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
  • Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
  • Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
  • Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Ceto Wasu Daliban St. Mary’s Tsaro
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
  • CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.