Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika

Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe
Published: July 29, 2026 at 10:55 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta jihar Gombe (GOSERC) ta gudanar da wani muhimmin taro da mahukuntan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Savannah, a wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa domin inganta rabon wutar lantarki a faɗin Jihar Gombe.

Da yake zantawa da Manema labarai bayan kammala taron, Shugaban Hukumar, Dakta Usman Abba Arabi, ya bayyana cewa manufar taron ita ce samar da dabarun haɗin gwiwa da za su tabbatar da inganta samar da wutar lantarki ga al’ummomin jihar.

Ya ce Gwamnatin jihar Gombe ce ta kafa Hukumar GOSERC domin tsara da kuma sa ido kan harkokin kasuwar wutar lantarki a yankunan karkara da birane, tare da tabbatar da cewa masu amfani da wutar lantarki sun samu ingantaccen sabis.

Dakta Usman Abba Arabi ya jaddada cewa Hukumar za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata, yana mai bayyana fatan cewa nan ba da jimawa ba al’ummar jihar za su fara cin gajiyar ingantacciyar, tabbatacciya kuma mai sauƙin samu ta fuskar farashi.

A nasa jawabin, Jagoran Tawagar Kamfanin Savannah Electricity Distribution Company, Abiddeen Olariwaju, ya bayyana cewa kamfanin sabon reshe ne na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED), wanda aka kafa bayan fara aiki da Dokar Wutar Lantarki ta shekarar 2023, wadda ta bai wa jihohi damar tsara da gudanar da kasuwar wutar lantarki a yankunansu.

Olariwaju ya ce kamfanin ya tanadi tsare-tsare na gajeren lokaci, matsakaicin lokaci da kuma na dogon lokaci domin bunƙasa samar da wutar lantarki a Jihar Gombe.

Ya ƙara da cewa an riga an fara gyaran na’urorin rarraba wutar lantarki (transformers) a garin Bajoga, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Funakaye, da kuma wasu sassa na cikin birnin Gombe, a matsayin matakin farko na aiwatar da shirin.

Ya tabbatar da cewa kamfanin zai ci gaba da aiki tare da Hukumar GOSERC da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga daukacin al’ummar jihar Gombe.

Har ila yau, Olariwaju ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa rattaba hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta jihar Gombe, yana mai cewa hakan ya sanya Gombe cikin jihohi goma na farko a Najeriya da suka kafa cikakkiyar hukuma mai kula da harkokin wutar lantarki a matakin jiha.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji
Next Post: Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati

Karin Labarai Masu Alaka

Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi Afrika
Shugaban Ƙasar Djibouti Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Afrika
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Alejandro Balde Na Dab Da Komawa Manchester United Daga Barcelona
  • Kocin Newcastle Matthias Ya Ce Lewis Hall Ba Zai Koma Manchester United Ba
  • Dan Wasan Baya Na Chelsea, Disasi, Zai Yi Gwajin Lafiyarsa A Crystal Palace
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai
  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Galatasaray Ta Yi Watsi Da Tayin €150m Daga Al-Hilal Kan Victor Osimhen Wasanni
  • Jam’iyyar ADC Ta Karbi Peter Obi Da Wasu Manyan ‘Yan-Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Haryanzu Abubakar Malami Da Dansa Suna Hannun Hukumar EFCC Labarai
  • Zaben Osun 2026: Darasi Ga APC, Gargadi Ga ADC, Nasara Ga Adeleke Afrika
  • Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
  • Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.