Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya
Published: January 20, 2026 at 4:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya kammala ziyara ta biyu ta shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Ziyarar ta gudana daga 4 zuwa 19 ga Janairu, 2026, inda aka mayar da hankali kan ƙarfafa tsare-tsaren aiki, da inganta haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya, tare da daidaita masu ba da hidima daga Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki domin su dace da ka’idoji da jadawalin Saudiyya.

A sanarwar da Ahmad Muazu, mataimaki na musamman ga shugaban NAHCON kan yaɗa labarai ya fitar a ranar Talata, yayin ziyarar, tawagar NAHCON ta gana da manyan hukumomi, da suka haɗa da Ma’aikatar Hajji da Umrah, Hukumar Jiragen Sama (GACA), Ma’aikatar Lafiya, da masu kula da Mashā’ir, masauki da abinci, jiragen sama, da ‘yan Najeriya mazauna Saudiyya, da tsarin huldar kafafen yaɗa labarai.

Daga cikin manyan nasarorin da aka cimma; akwai kulla yarjejeniyoyin hidima, ɗora kwangiloli da jadawalin jirage a dandalin Nusuk Masar, duba asibitoci a Makkah da Madinah, tabbatar da ƙa’idar gwajin lafiya, da daidaita tsarin na’urorin dijital da aiki.

NAHCON ta kuma yi taro da hukumar kula da alhazai ta jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido, domin ƙarfafa aiki a kan lokaci, ƙa’idoji da ingancin hidima kafin Hajjin 2026.

Hukumar ta ce yanzu za ta shiga mataki na gaba na shiri, ciki har da kammala kwangiloli, ɗora bayanan maniyyata, da ci gaba da haɗin gwiwa domin tabbatar da Hajji mai sauƙi kuma cikin tsari.

Labarai

Post navigation

Previous Post: CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya
Next Post: Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB

Karin Labarai Masu Alaka

Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai
Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai
Iran Tana Duba Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Amurka Afrika
Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Adamu: “Yakar Cin Hanci Daga Tushe Itace Mafita Daya Tilo” Labarai
  • Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
  • Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
  • Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.