Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Iran Zata Kai Hari Tashar Makamashin Ruwa A Gulf
Published: March 23, 2026 at 7:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A jiya Lahadi Iran ta bayyana cewa za ta kai hari kan tashar makamashi da na ruwa na ƙasashen maƙwabta a yankin Gulf, a matsayin martani idan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya aiwatar da barazanar da ya yi na kai hari kan tashar wutar lantarki na Iran cikin sa’o’i 48, lamarin da ke ƙara tsananta rikicin da ya shafe makonni uku yana gudana.

Hasashen irin waɗannan hare-hare na ramuwar gayya kan kayayyakin more rayuwa na fararen hula na iya ƙara tsananta rikicin yankin, tare da girgiza kasuwannin duniya lokacin da za su sake buɗewa a safiyar Litinin.

An ji ƙararrawar gargadin hare-haren sama a sassan Isra’ila tun daga farkon safiyar Lahadi, domin sanar da zuwan makamai masu linzami daga Iran, bayan da mutane da dama suka jikkata a daren jiya sakamakon hare-hare biyu daban-daban a garuruwan Arad da Dimona da ke kudancin Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun ce bayan wasu sa’o’i sun fara kai hare-hare kan Tehran a matsayin martani.

Trump ya yi barazanar a daren jiya cewa zai “lalata gaba ɗaya” tashoshin samar da wutar lantarki na Iran idan Tehran ba ta buɗe mashigin ruwan Hormuz gaba ɗaya cikin sa’o’i 48 ba. Wannan na zuwa ne kusan kwana guda bayan ya yi magana kan “rage zafin yaƙin.” Ya kuma yi wannan sabuwar barazana ne a daidai lokacin da dakarun ruwan Amurka da manyan jirage masu sauka cikin ruwa ke kan hanyarsu zuwa yankin.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya
Next Post: An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC

Karin Labarai Masu Alaka

Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine Labarai
Wani Abu Ya Fashe A Asibitin Bagudo Dake Jihar Kebbi Tsaro
Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Tinubu Zata Gyara Hanyar Akwanga Zuwa Jos Labarai
  • Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
  • Tawagar IMF Tana Kasar Kenya Domin Tattauna Bada Lamuni Labarai
  • An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba. Afrika
  • Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka Amurka
  • Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.