Isra’ila zata mamaye Lebanon har zuwa gabar kogin Litani, yankin da Ministan tsaron kasar, Isra’ila Katz, ya fada ranar talata a zaman “yankin tsaro,” wadda shine a karon farko, da bani yahudun ta fito fili da nufin kasar na mamaye kusan kashi 10 cikin dari na Lebanon.
A wani taro da babban hafsan hafsoshin kasar, Katz, yace sojojin kasar za su ci gaba da iko kan sauran gadoji da suke yankin har zuwa kogin Litani, kogin da ya hade da na Nilu, kimanin kilomita 30 daga kan iyakan Isra’ila.
Kungiyar Hezbollah mai samun goyon baya daga Iran, tace zata yi yaki domin hana Isra’ila mamayar kudancin Lebanon, ta kira matakin a zaman mummunar barazana ka diyaucin kasar.


