Jami’an Amurka da ke mayar da martani kan rashin tabbas na tattalin arziki kan hauhawar farashin man fetur, a ranar Lahadi sun yi hasashen cewa, yakin Amurka da Isra’ila zai kawo karshe nan da makwanni, kuma za a samu raguwar farashin makamashi, duk kuwa da ikirarin da Iran din ta yi na cewa tana nan daram da karfi kuma a shirye take ta kare kanta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai karin hare-hare kan babbar cibiyar fitar da man fetur ta Iran a tsibirin Kharg a karshen mako, ya kuma ce bai shirya cimma matsaya ba don kawo karshen yakin da ya rufe mashigin Hormuz mai matukar muhimmanci tare da girgiza kasuwannin makamashi na duniya.
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa, a farkon wannan makon ne gwamnatin Trump ta shirya yin shelar cewa kasashe da dama sun amince da kafa wata kawance don raka jiragen ruwa ta mashigin ruwa amma har yanzu suna tattaunawa kan ko za a fara gudanar da ayyukan, kafin ko bayan an kawo karshen tashin hankali, in ji jaridar Wall Street Journal, inda ta ambato wasu jami’an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba, Sai dai Fadar White House ba ta amsa bukatar jin ta bakin nata ba.
Trump, wanda a ranar Juma’a ya ce sojojin ruwan Amurka “nan ba da jimawa ba” za su fara rakiyar jiragen dakon mai, ya ce Iran na son yin shawarwari, amma ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi a ranar Lahadi ya musanta wannan ikirarin.


