Ƙananan hukumomi na neman karɓar kuɗaɗensu kai tsaye yayin da jihohi suka riƙe N7.43tn
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE) sun bayyana cikakken goyon bayan su ga shirin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya (FAAC), duk da cewa gwamnatocin jihohi na ci gaba da riƙe iko kan rarraba kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
A yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 15 na jam’iyyar APC da aka gudanar a Babban Dakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su mutunta hukuncin Kotun Ƙoli da ya ba wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kan su ta fuskar kuɗi.
Shugaban ya yi gargaɗin cewa idan gwamnonin suka ƙi bin hukuncin, zai iya fitar da umarnin shugaban ƙasa (Executive Order) domin tabbatar da cewa ana tura kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga FAAC zuwa asusun su.
Wannan jawabi na Tinubu ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 11 ga Yuli, 2024, wanda ya goyi bayan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar domin tilasta ‘yancin kuɗi ga ƙananan hukumomi.
A hukunci ɗaya tilo, kwamitin alkalai bakwai na Kotun Ƙoli ya ayyana cewa ba a bisa doka ba ne gwamnatocin jihohi ke riƙe ko sarrafa kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi.
Kotun ta kuma ce kafa kwamitocin rikon ƙwarya (caretaker committees) na nufin jihohi suna ƙwace ikon ƙananan hukumomi, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999.
Sai dai duk da shafe watanni 18 da yanke hukuncin, binciken majiyar mu ya nuna cewa har yanzu ba a aiwatar da shi yadda ya kamata ba.
Har yanzu ana ci gaba da tura kuɗaɗen ƙananan hukumomi ta hannun gwamnatocin jihohi, lamarin da ke haifar da jinkiri da saɓani tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN), gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi da sauran hukumomi.
Bincike ya nuna cewa gwamnatocin jihohi sun ci gaba da sarrafa ƙalla Naira tiriliyan 7.43 da aka ware wa ƙananan hukumomi daga Yuli 2024 zuwa Disamba 2025, duk da hukuncin Kotun Ƙoli da ya umurci biyan kuɗin kai tsaye.
Binciken rabon kuɗaɗen FAAC ya nuna cewa an ware wa ƙananan hukumomi N7.43tn a cikin watanni 18, daga Yuli zuwa Disamba 2024 da kuma duk shekara ta 2025, duk da cewa tsarin biyan kuɗin kai tsaye bai canza sosai ba.
A rabin shekarar 2024 na biyu kadai, ƙananan hukumomi sun karɓi N2.08tn, yayin da adadin ya tashi zuwa N5.35tn a shekarar 2025.
Duk da ƙarin kuɗaɗen shiga, ana ci gaba da biyan su ne ta tsohon tsarin Asusun Haɗin Gwiwar Ƙananan Hukumomi da jihohi (State Joint Local Government Account), wanda ke bai wa gwamnonin jihohi cikakken tasiri kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
A wata hira da aka yi da shi a Abuja, Babban Sakatare na ALGON, Muhammed Abubakar, ya tabbatar da goyon bayan ƙungiyar ga shirin Shugaba Tinubu na tilasta cire kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga FAAC.
Muhammed ya ce Shugaban Ƙasa ya gargaɗi gwamnoni kai tsaye, kuma ya jingina hakan ne da hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya bayyana a matsayin hukumar shari’a mafi ƙololuwa a ƙasar nan.


