Morocco ta kwashe ‘yan kasar fiye da su dubu 140, daga yankunan kasar da suke fuskantar bala’in ambaliya, tare da kara kira ga mazauna sassar kasar da ba tare da bata lokaci ba su bar yankunan, ganin yadda koguna suka cika suna batsewa, ci gaba da ruwan sama, wadda ya tilastawa madatsun ruwa su saki ruwa.
Ana amfani da jirage masu saukar ungulu domin aikin ceto, yayinda karin ruwa ya mamaye wurare masu yawa a fadin arewa maso yammacin kasar. Tun a ranar jumma’ar makon jiya ne hukumomin kasar suka tura sojoji domin su taimakawa aikin kwaso jama’a, yayinda ake kara samun bayanai na samun karin ruwan sama a makon nan.
A Moroccon an sami karin ruwan-sama da ya kai kashi 215 cikin dari, idan aka kwatanta da bara. Wanda ya nuna karin ruwan saman da kamar kashi 54 cikin dari sama da abunda aka saba samu.


