Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Magoya Bayan Obi Sun Yi Tutsu Gabanin Zaben 2027
Published: March 21, 2026 at 4:08 AM | By: Nasiru Adamu Elhikaya | Updated: March 21, 2026

Manyan Magoya Bayan Obi Sun Fice Da Kafa Kungiyar Movement Nigeria

Wasu daga manyan jami’an siyasar dan takarar adawa a Najeriya wato Peter Obi sun barranta daga tafiyar da kafa wata kungiyar cimma sabon muradi don babban zaben 2027.

‘Yan siyasar sun koka cewa tafiyar ta su mai taken OBIDIENTS ta sauka daga kan manufofin kare martabar dimokradiyya

“A matsayinmu na masu tafiyar farar hula mun yi amanna cewa tsarin siyasa na cikin abubuwan da kan kawo cigaban kasa, za mu dage wajen hulda da wadanda su ka cancanta, cikin gaskiya da bin ka’ida ga sauran tafiyar dimokradiyya ko jam’iyyun siyasa. Wannan tafiya ce ta ma’aikata da ke fafutuka..” Inji madugun tafiyar mai taken MOVEMENT Nigeria Prince Kolade Ademola.

Ademola ya ce ba lallai a yanzu su na da wanda za su marawa baya ga babban zaben ba amma za su goyi bayan duk wanda su ka ga ya dace da tafiyarsu kuma ya karfafa cewa lokaci bai kure mu su ba.

‘Yan sabuwar tafiyar maza da mata sanya da riguna da hulunan hana-sallah masu tambarin kungiyar, na nuna rashin daidaito da tuntubar da ta dace ya sa su kaucewa tafiyar Peter Obi wanda ya zo na uku a yawan kuri’a a zaben 2023.

Mataimakin sakataren jam’iyyar LEBA na kasa wacce Obi ya yi ma ta takara Dokta Joseph Liran ya ce sam ba don dalilin kaurar Obi zuwa jam’iyyar ADC ya sa su barranta daga tafiyar ba “Obi ya na da ‘yancin shiga kowace jam’iyya mu ma mu na da namu ‘yancin”

Shi ma ma’ajin jam’iyyar LEBA Malam Hamisu Santuraki ya ce ba za su ce dole sai muradun LEBA za a bi ba a madadin ra’ayin jama’ar kasa.

Hakanan Santuraki ya ce sun kawo karshen takaddamar shugabancin jam’iyyar ta LEBA bayan hukuncin kotun koli da ya kawar da jagorancin Julius Abure.

Irin wannan tafiya ba sabon abu ba ne a shekarar siyasa inda ‘yan siyasar ke duba

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/OBIDIENTS-DUMP-OBI-START-NEW-MOVEMENT.mp3

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya
Next Post: Hawan Sallah Daga Masarautar Kaltungo

Karin Labarai Masu Alaka

INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
Iran Tace Jakadan Kasar Ta A Lebanon Zai Cigaba Da Zama A Beirut Afrika
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Ya Zamo Sakataren Jam’iya Mai Mulki Labarai
Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Bauchi Ta Amince Domin Inganta Kasuwancin Nama A Jihar Labarai
  • Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe Najeriya
  • Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya Tsaro
  • An Kashe Mayakan Sakai 67 A Pakistan Sauran Duniya
  • Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.