Najeriya ta yi zargin cewa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta sanya ‘yan wasa marasa cancanta a gasar cin kofin duniya
Najeriya ta mika takardar koke ga FIFA tana zargin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta sanya ‘yan wasa da basu cancantaba a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Afirka a shekara mai zuwa, in ji mai magana da yawun hukumar (NFF).
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta doke Najeriya a bugun fenariti a watan da ya gabata don ci gaba da rayuwa a fatanta na fitowa gasar a Arewacin Amurka, kuma za ta fafata a gasar share fagen shiga gasar tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a watan Maris inda kungiyoyi shida za su bi sahun matsayi biyu a gasar karshe ta kungiyoyi 48.

NFF ta ce ‘yan wasa da dama ‘yan kasa suna da takardadun izinin kasashe biyu sun bugawa DR Congo wasa ba tare da cika sharuddan da ake bukata ba.
“Dokokin Congo sun ce ba za ka iya samun ‘yan kasa biyu ba,” in ji babban sakataren NFF Mohammed Sanusi ga manema labarai.
“Akwai da yawa daga cikinsu da ke da fasfo na Turai, wasu daga cikinsu fasfo na Faransa, wasu kuma fasfo na Holland.
“Dokokin FIFA sun ce da zarar ka mallaki fasfo na kasarka, ka cancanta.
A ganinmu, sun cancanci hakan ne ya sa FIFA ta wanke su.
“Amma hujjarmu ita ce an yaudari FIFA har ta wanke su domin ba alhakin FIFA ba ne ta tabbatar da cewa an bi ƙa’idodin Congo.”
“FIFA tana bin ƙa’idodinta ne, bisa ga abin da aka gabatar wa FIFA ne ya suka wanke su, mu a wajanmu muna cewa an yi zamba ne.”

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo ta yi watsi da zarge-zargen da ake ma ta.
“Idan ba za ku iya cin nasara a filin wasa ba, to kada ku yi ƙoƙarin cin nasara daga ƙofar baya,” in ji Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kongo (Fecofa) a wani rubutu da ta yi a shafukan sada zumunta.
“Dole ne a buga gasar cin kofin duniya da mutunci da kwarin gwiwa. Ba tare da dabaru na shari’a ba da ku kawo shi.”
FIFA ba ta amsa buƙatar yin tsokaci nan take ba saboda lokutan aiki.
Gasar cin kofin duniya za ta gudana a Amurka, Kanada da Mexico daga 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli.


