Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe Afrika
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Ƙarfafa Matakan Kare Dabbobi Daga Cututtuka Afrika

NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi
Published: June 30, 2026 at 4:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin magance abin da ta bayyana a matsayin hare-haren nuna wariya da kuma tauye haƙƙin Musulmi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Majalisar ta bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba cikin gaggawa, hakan na iya haifar da ƙarin damuwa da rashin gamsuwa a tsakanin al’ummar Musulmi.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na NSCIA, Abbas Jimoh, ya fitar a madadin majalisar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi na Najeriya, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

A cikin sanarwar, majalisar ta nuna damuwa kan abin da ta ce na ci gaba da faruwa na nuna wariya ga Musulmi da kuma tauye musu wasu haƙƙoƙi da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar.

NSCIA ta jaddada cewa Najeriya ƙasa ce da ke bai wa kowane ɗan ƙasa damar gudanar da addininsa cikin walwala da ‘yanci, don haka ya zama wajibi gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da kare waɗannan haƙƙoƙi ba tare da nuna bambanci ba.

Majalisar ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike kan duk wasu korafe-korafe da suka shafi tauye ‘yancin addini tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da adalci da zaman lafiya.

NSCIA ta ce tana sa ran gwamnati za ta yi abin da ya dace cikin gaggawa domin kare haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa, tare da tabbatar da cewa an mutunta haƙƙin kowane ɗan ƙasa ba tare da la’akari da addininsa ko asalinsa ba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe
Next Post: An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
Amurka Na Gargadin Rwanda Da Ta Mutunta Alkawali Afrika
Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
Sauyin Yanayi: Masana A Kaduna Sunyi Kira Ga Yan Kasuwa Su Mayar Da Shara Zuwa Kudi Afrika
Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Taki Da Mai Ga Manoma Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai Afrika
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.