Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba
Published: March 10, 2026 at 4:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani rahoton bayanan leken asiri na Amurka da aka rubuta shi jim kadan kafin Amurka da Isra’ila su far ma kasar Iran da hare-hare, ya cimma daidaito a kan cewa hare-haren sojan Amurka ba zasu iya kawo sauyin shugabanci a kasar ba.

Wasu majiyoyi biyu da suka ga wannan rahoton da hukumomin leken asirin Amurka karkashin inuwar Majalisar Ayyukan Leken Asiri ta kasa suka rubuta a cikin watan Fabrairu, sun ce rahoton ya tsayar da shawarar cewa kai hare-hare ta sama ko kuma jimawa ana kai wadannan hare-haren, zai yi wuya su haifar da sabuwar gwamnati a Iran.

Majiyoyin suka ce rahoton ya ce koda an kashe dukkan shugabannin kasar na yanzu, zai yi wuya a iya canja gwamnatin kasar.

Wannan bayanin, ya gurgunta ikirarin da gwamnatin shugaba Trump take yi cewa zata iya cimma burinta na kai farmakin kan Iran cikin kankanin lokaci.

Mutanen biyu, wadanda suka bukaci da a sakaye sunayensu sun fada ma kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa hukumomin leken asirin na Amurka sun cimma daidaito kan cewa babu wasu ‘yan adawa dake da karfi ko hadin kan da zasu iya karbar mulki a kasar Iran ko da an kashe shugabannin kasar.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaban Kasar Madagascar Ya Kori Prime Minista Da ‘Yan Majalisa
Next Post: Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata

Karin Labarai Masu Alaka

Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
Shugaban Kasar Amurka Yakara Hana Wasu Kasashe Shiga Amurka Ciki Harda Nijar Amurka
Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
Rundunar Tsaron Haɗin Gwiwa Ta Arewa Maso Gabas Ta Kashe Fiye Da ‘Yan Ta’adda 438 Labarai
Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
Farashin Danyen Mai A Amurka Ya Tashi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
  • Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda Siyasa
  • Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
  • Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba Labarai
  • Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Karu A Karshen 2024 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.