Rundunar sojojin Iran ta ce an kashe mutane akalla 104, wasu 32 kuma sun ji rauni a harin da Amurka ta kai kan wani jirgin ruwan yaki na Iran cikin makon da ya shige a dab da gabar kasar Sri Lanka.
A ranar laraba wani jirgin karkashin ruwa na Iran ya nutsar da jirgin ruwan yakin kasar Iran mai suna Dena, kimanin mil 19 daga tashar jiragen ruwan Galle na kasar Sri Lanka, ya kashe mayaka da yawa dake cikin jirgin.


