Shugaba Donald Trump na Amurka ya hada kan shugabannin Kwango ta Kinshasa da Rwanda domin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya jiya alhamis birnin Washington, duk da cewa har yanzu ana can ana ci gaba da gwabza fada a yankin da ya jima yana fama da fitina.
Shugaba Paul Kagame na Rwanda da shugaba Felix Tshisekedi na Kwango sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kan tattalin arziki da aka cimma a watan da ya shige, da kuma yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka da Qatar suka kulla tsakanin sassan biyu a watan Yuni.
Har ila yau an shirya cewa zasu sanya hannu a kan wata yarjejeniyar game da muhimman ma’adinai.
Rattaba hannu kan yarjejeniyar ta bawa shugaba Donald Trump na Amurka wata sabuwar nasarar da aka ce ba ta zahiri ba, a kokarinsa na nuna cewa shi mai kokarin wanzar da zaman lafiya ne, a wannan karon a saboda har yanzu ana zub da jini a wannan yakin da aka ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshensa.
Amurka tana kwadayin sanya hannunta a kan ma’adinai masu muhimmanci da yawa da kasar Kwango take da su, kuma tana ta kokarin dakile fintinkau da kasar China ta yi a fannin samo irin wadannan ma’adinai a fadin duniya.
A yayin da shugabannin kasashen biyu ke rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya, an bada rahoton gumurzu a tsakanin’yan tawayen kungiyar M23 da Rwanda ke goyon baya da sojojin gwamnatin Kwango a lardin Kivu ta Kudu.
Wani kakakin kungiyar M23 ya zargi sojojin gwamnati da laifin cilla bama bamai a kan yankunan fararen hula.
Masu fashin baki sun ce tsoma bakin Amurka a cikin lamarin ya dakile yaduwar fadan, amma kuma bai iya warware muhimman batutuwan da suka janyo wannan yakin ba.


