Shugaban kasar Ukrain, Volodymr Zelensky yana so ya tattauna kan batutuwan da suka Shafi yankunan kasar da shugaban Amurka Donald Trump, wadanda su ne manyan abubuwa da suke kawo cikas wajen kawo karshen yakin ta da kasar Rasha.
Shugabannin biyu zasu tattauna ne a jihar Florida ranar Lahadi, a yayin da aka kusa karkare shirin zaman lafiya mai matakai ashirin, da kuma tabbatar da tsaro.
Da yake sanar wa da manema labarai kan batun tattaunawar, Zelensky ya ce za’a iya cimma matsaya da dama kafin zuwan sabuwar shekara, saboda fadar Washington ta zage dantse wajen ganin ta kawo karshen yaki gadan-gadan da Rasha ke yi da Ukrain, wanda ya kasance mafi muni a tarayyar turai tun bayan yakin duniya na biyu.
Israela ta kasance kasa ta farko da ta amince da Jamhuriyar Somaliland, da ta ayyana kan ta a matsayin kasa me cin gashin kan ta, ranar Jumu’a kuma wannan kuduri zai iya sauya fasalin dabi’un yankuna, kuma zai kawo kalubale ga ra’ayin Somalia na rashin son a warewa
Fira minista Benjamin Netanyahu, ya ce Israila zata nemi hadin guiwa da Somaliya a harkar noma, lafiya, fasaha da kuma tattalin arziki kuma a wani jawabi ya taya shugaban Somaliya Abdulrahman Muhammad Abdullahi murna, tare da yaba yadda yake gudanar da mulkin sa, ya kuma gayyace shi ya kai ziyara Israil.
Netanyahu ya ce wannan furuci, na daga cikin tsarin hadakar yankuna na Abraham Accords, wanda aka rattaba hannu a kai bisa ga shawara shugaba Donald Trump.
An kulla yarjejeniyar ne da aka tsara a shekarar 2020, lokacin mulkin Trump na farko, kuma ta kunshi kasar Isra’ila ta yi huldar diplomassiya bisa ka’ida da kasashen hadaddiyar daular larabawa, da Bahrain, tare da wasu kasashen da suka hadu daga baya.


