Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar
Published: January 24, 2026 at 7:31 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban kasar Ivory coast  Allassane Ouattara yayi garambawul ga majalisar ministocin kasar, inda ya daukaka kani ko dan’uwansa wanda shine ministan tsaro, yanzu ya sami karin mukami na zama mukaddashin PM kasar. Tene Birahima Ouattara, zai kuma ci gaba da rike mukaminsa na ministan tsaro.

Wannan mataki ya kara daukaka kanin na sa kan madafun iko, yayinda sauran ministoci kowa yana daram kan kujerarsa.

Garambawul din nan ya biyo bayan nasarar sake cin zabe da shugaba Ouattara yayi cikin watan Oktoba, da kuma nasarar jam’iyyarsa na samun rinjaye a zaben majalisar dokokin kasar da aka yi cikin watan Disamba bara.

Shugaba Ouattara dan shekaru 84 da haifuwa, wanda tsohon mataimakin darektan asusun bada lamuni na duniya da aka fi sani da lakabin IMF, yana jan ragamar kasarsa tun a shekara ta 2011, yace yana so ya share fage ga sabbin jini da za su shugabanci kasar tun yana kan mulki.

Wadan nan sauye sauye suna zuwa ne a lokacin da Ivory Coast, kasar da Allah Ya yiwa albarkar Cocoa fiye da ko wace kasa a duniya ta kokarin ta kara zugu kan ci gaban tattalin arziki na tsawon shekaru 15, wadda yasa kasar ta zama wacce tattalin arzikinta yafi bunkasa a yankin baki daya.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP
Next Post: Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa

Karin Labarai Masu Alaka

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
Magoya Bayan Dan Hamayya A Afirka Ta Kudu Sun Hallara A Kotu Afrika
Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa Siyasa
Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya Wasanni
  • Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
  • Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan Labarai
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
  • Jami’an Shiga Da Fice A Afirka Ta Kudu Sun Tafka Badakalar Kudade Afrika
  • Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran Afrika
  • Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.