Rundunar sojojin Amurka ta ce ta kai hari a kan wani karamin jirgin ruwan da ake zargin na safarar muggan kwayoyi ne a yankin ruwa na kasa da kasa a gabashin tekun Pacific jiya alhamis, ta kashe mutane hudu.
Rundunar sojojin ta Amurka, ta fada cikinwata sanarwar da ta bayar a dandalin sada zumunta na X cewa bayanan leken asiri sun tabbatar da cewa jirgin ruwan yana dauke da muggan kwayoyi, kuma an kai masa hari a kan hanyar da masu safarar muggan kwayoyi suka saba bi a gabashin tekun Pacific.
A halin da ake ciki, ‘yan majalisar dokokin Amurka sun samu ganin takardar dake kunshe da takaitaccen bayani da ya tsara matakan da gwamnatin Trump take dauka na kai hari kan jiragen ruwan da ake zargin suna dauke da kwayoyi a tekun Pacific.
‘Yan majalisar suna daukar wannan takarda a zaman mai muhimmanci ga binciken da suke yi na wani harin da sojojin Amurka suka kai kan wani jirgin a ranar 2 ga watan Satumba, inda suka kashe mutane 11, cikinsu har da wasu mutane biyu da suka kubuta da rai daga harin farko da aka kai kan jirgin.
Wannan takardar da ta takaita bayanin tana dauke da shafuka biyu, kuma ta zayyana jerin masu bayarda umurni, da yadda gwamnatin Trump take amfani da bnayanan leken asiri wajen gano irin wadannan jirage.
‘Yan majalisar sun bukaci da a kawo musu cikakkiyar takardar wadda ke dauke da bayanin komai da komai game da hare-haren, amma ba a san ko ma’aikatar tsaro zata yarda su gani ba.
A halin da ake ciki dai, manyan ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar dokoki dake cikin wadanda aka yi ma bayanin wasu hare-haren da aka kai a tekun Caribbean sun fada jiya alhamis cewa hankulansu sun tashi da bidiyon da suka gani na wasu mutane biyu da suka kubuta da rai, amma sai aka kara kai musu hari aka kashe su, Sai dai kuma takwarorinsu na Republican sun kare wannan hari na biyu da cewa bai saba ma doka ba.
Babban dan jam’iyyar Democrat a kwamitin kula da ayyukan leken asiri a majalisar wakilai, Jim Himes yace sun ga mutane biyu wadanda ba su da wata hanyar da zasu iya zuwa wani wuri, da jirginsu da aka gama lalatawa, amma sai aka kashe su.
Yace wannan abu na daya daga cikin abubuwa mafi tashin hankali da ya gani.
Shi ma babban dan Demicrat a kwamitin kula da ayyukan soja na majalisar dattijai, Jack Reed, yace hankalinsa ya tashi matuka da wannan bidiyo da ya gani kuma ya kamata a sake shi jama’a su gani.
Amma kuma shugaban kwamitin ayyukan leken asiri na majalisar dattijai dan jam’iyyar Republican, Tom Cotton, cewa yayi shi abinda ya gani mutanen biyu suna kokarin su juya jirginsu da ya kife ne, dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka domin su ci gaba da fafatawa.


