Ganin yadda rabuwar kawunan al-uma da banbance banbance awarewacin Najeriya ke kara rura wutar matsalar tsaro ya sa kungiyoyin yankin hada wata sabuwar kungiyar sulhu da sasanta juna domin hada kan al-umar yankin da nufin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da riki tsakin al-umomin yankin baki daya.
Sabuwar kungiyar sulhu da hada kawunan al-uma a arewacin Najeriyan da ke karkashin Jagorancin tsohon mai-baiwa shugaban kasa shawara kan ta harkokin siyasa a offishin mataimakin shugaban kasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ta hada da kungiyar musulmin Najeriya ta Jama’atu Nasrul-Islam da kuma ta Kiristoci CAN da sauran kungiyoyin arewa kuma a jiya Laraba kungiyar ta fara ziyarar hada kawunan al-umar yankin baki daya.
Daga Kaduna, Wakilin mu Isah Lawal Ikara ya bi tawagar kungiyar zuwa ofisoshin kungiyar Jama’atu Nasrul-Islam da kuma Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN, kuma ga rahoton da ya aiko mana……
Rashin jituwa tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista da kuma maganar matsalar tsaro da talauci dai na cikin manyan matsalolin dake damun yankin arewacin Najeriya, harma wasu na ganin hakan ne ya sa shugaba Donald Trump na Amurka barazar aike sojoji yankin da sunan yakar ‘yan-ta’adda. Sai dai shugaban wannan kungiya ta sulhu Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce kungiyar ta shirya share wannan damuwa dake damun Arewa.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Arewaci Rebaren Joseph John Hayaf ya ce gaske an sami baraka tsakanin al-umar arewa a baya amma yanzu an gano bakin zaren.
Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasrul-Islam na Kasa Farfesa Khalid Aliyu Abubakar ya ce Arewa ta gane ciwon da ke damun ta kuma ta samu magani.
Game da banbancin wannan sabuwar kungiyar sulhu da sauran kungiyoyin da aka kafa da irin wadan nan manofofi a arewa kuwa, Rebaren Joseph John Hayaf ya ce ita wannan sabuwar kungiyar hadaka ce ta dukkan manyan kungiyoyin arewacin Najeriya.
Arewacin Najeriya dai ya sha fara da rikice-rikicen addini da na kabilanci wanda wasu ke ganin matsalar tsaron dake damun yankin ma ana shafa mata addini da kabilanci duk lolacin da ‘yan-ta’adda ko ‘yan-bindiga su ka kashe mutane. Abun jira a gani kuma shine, shin wannan sabuwar kungiyar za ta iya magance wannan matsalar da ta ki-ci ta-ki cinyewa.


