Ukraine ta tura wata tawagar kwararru zuwa Qatar, da hadaddiyar daular larabawa, da Saudiyya, domin su taimaka musu su kare haren haren da Iran take kai musu, inji shugaban Ukraine Vladimir Zelensky a bayani da yayi ranar talata.
Kasashe da suke yankin Gulf, sunyi amfani da makamai masu linzami masu tsada domin kakkabo jiragen yaki da basu da matuka da Iran take harbawa kuma masu saukin kudi, saboda haka suka nemi taimakon Ukraine wacce kullum take yakar irin wadan nan jiragen drones da Rasha take kaiwa Kyiv farmaki da su. Zelensky, bai bada wani karin bayani kan tawagar ba, sai dai yace dukkan su za su kai can cikin makon nan


